"Atiku da Obi Suyi Koyi da Jonathan ta Hanyar Kiran Wayar Tinubu Su Tayashi Murna" - Kwamitin Neman Zaɓen APC

"Atiku da Obi Suyi Koyi da Jonathan ta Hanyar Kiran Wayar Tinubu Su Tayashi Murna" - Kwamitin Neman Zaɓen APC

  • Tinubu Yayi Nasarar Lashe Jahohi 12 Sannan Kuma ya Samu Kaso 25 a Cikin 100 Na Kuri'un da aka Kaɗa a Jihohi da Yawa Kamar Yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya Tanadar.
  • A Shekarar 2015, Shugaban Ƙasa Jonathan Bai Jira INEC ta Gama Tattara Sakamakon Zaɓuka ba, ya Kira Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya Taya shi Murna.
  • Kungiyar Tayi Martani Mai Zafin Gaske ga Waɗanda Sukaita Kira ga Shugaban INEC Mahmood Yakubu Akan ya Ajiye Aikin sa

Abuja - Anyi Zaben shugaban ƙasa dana yan majalisa, an gama tattara sakamakon daya bada damar faɗin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

A wannan ƙaron, cikin yan takarkari huɗu, da suka haɗa da Atiku Abubakar na PDP, Bola Ahmed Tinubu na APC, Peter Obi na LP da Rabi'u Kwankwaso mutum ɗaya ne yayi nasara.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Fadi Zaben Zama Sanatoci A Zaɓukan 2023

Wannan ba wani bane face Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC. Kamar ko wani irin zaɓe wannan an cigaba da kiranye kiranye ga yan takarkaru.

Jagaban
Bola Ahmed Tinubu: Zababben Shugaban Kasa Hoto: Thecable.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ne yasa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC yayi kira ga ƴan takarar jam'iyyar LP Peter Obi da Atiku Abubakar na PDP da su amshi faɗuwa su fito fili su kira Bola Tinubu domin taya murnar nasarar da yayi akan su.

Dele Alake, shine mai bawa ƙungiyar shawara akan kafofin yaɗa labarai, kuma shine ya shaidawa manema labarai a talatar nan data gabata a garin Abuja.

A jiya ne dai aka kammala tattara sakamakon zaɓe na ko ina dake ƙasar nan a Abuja.

Inda Tinubu yayi nasarar lashe jahohi 12 sannan kuma ya samu kaso 25 a cikin 100 na kuri'un da aka kaɗa a jihohi da yawa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

Jaridar the Cable ta ruwaito yadda ɗan takarar jam'iyyar SDP yace, Atiku Abubakar da Obi ya kamata su nuna halin dattako wajen kiran Tinubu su tayashi murna sannan su amshi faɗuwa.

Da yake hira da manema labarai, Alake yace, idan yan takarar guda biyu suka bi sahun tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan sanda ya taya Muhammadu Buhari murna a 2015, tun kafin a faɗi wanda yayi nasara hakan ba gazawa bace.

"Muna kira ga Atiku Abubakar da Peter Obi da kakkausar murya da suyi koyi da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ta hanyar yadda da faɗuwa," Inji shi.

Ya ƙara da cewa:

"Zaɓen nan ɗan takarar mu ya daɗe da samun nasara domin sakamakon ya nuna tun a wajen tattaro sakamako na jihohi.

Yaci gaba da cewa:

" A shekarar 2015, Shugaban Ƙasa Jonathan bai jira INEC ta gama tattara sakamakon zaɓuka ba, ya kira shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya shi murna. Wannan shine halayyar da aka sani ta demokradiyya da kuma nuna dattaku.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Manyan Dalilai 4 Da Suka Sanya Atiku Abubakar Yasha Tumurmusa a Hannun Tinubu

"Saboda haka ne muke kira ga Atiku Abubakar da Peter Obi suma su biyo sahun hanyar daraja, maimakon ƙoƙarin ɗumama yanayin siyasa ta hanyar kalamai masu bijirowa mutane fushi. Atiku da Obi ku kira Tinubu tun yanzu don Allah".

Da yake nashi jawabin, Festus Keyamo wanda yake mai magana da yawun ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, yayi martani ne mai zafin gaske ga waɗanda sukaita kira ga shugaban INEC Mahmood Yakubu akan ya ajiye aikin sa.

Keyamo ya jaddada musu cewar, abune wanda ba daidai ba ga wani mutum ko jam'iyya su nemi a canja yanayin da ake gudanar da zaɓe tun kafin a saki sakamako na ƙarshe.

Ana tsaka da haka ne sai aka jiyo Tinubu yana yiwa ƴan Najeriya Wani Babban alƙawari.

Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya Babban Alkawari A Jawabinsa Bayan Lashe Zabe

Jim kaɗan da sanar dashi a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaɓukan, yayi kira ga jam'iyyun adawa da masu sukar sa da su hada hannu da shi don ciyar da kasar gaba.

Sannan yace, "Mu hada kai muyi aiki tare. Nayi alkawari zan yi aiki da ku,''

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida