Daga Ekiti Zuwa Zamfara: Sakamakon Zabe Daga Jihohin da Bola Tinubu Ya Lashe
A ranar 1 ga watan Maris ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben bana.
Tinubu ya zama zababben shugaban kasan Najeriya ne da kuri’u 8,794,726, kamar yadda shugaban inec, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da sanyin safiyar yau.
Yayin da masu murna ke murna, masu bakin ciki ke kokawa, Legit.ng Hausa ta tattaro muku dalla-dalla jihohin da Tinubu ya lashe zabe, da kuma adadin kuri’un da ya samu.
Jihohin da Tinubu ya lashe zabe da kuma kuri’un da ya samu:
1. Jihar Rivers
APC - 231,591
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
LP - 175,071
NNPP - 1,322
PDP - 88,468
2. Jihar Borno
APC - 252,282
LP - 7,205
NNPP - 4,626
PDP - 190,921
3. Jihar Zamfara
APC - 298,396
LP - 1,660
NNPP - 4,044
PDP - 193,978
4. Jihar Kogi
APC - 240,751
LP - 56,217
NNPP - 4,238
PDP - 145,104
5. Jihar Benue
APC - 310,468
LP - 308,372
NNPP - 4,740
PDP - 130,081
6. Jihar Niger
APC - 375,183
LP - 80,452
PDP - 284,898
NNPP - 21,836
7. Jihar Jigawa
APC - 421,390
LP - 1,889
NNPP - 98,234
PDP - 386,587
8. Jihar Oyo
APC - 449,884
LP - 99,110
NNPP - 4,095
PDP - 182,977
9. Jihar Ogun
APC - 341,554
LP - 85,829
NNPP - 2,200
PDP - 123,831
10. Jihar Ondo
APC - 369924
LP - 44405
NNPP - 930
PDP - 115463
11. Jihar Kwara
APC - 263572
LP - 31166
PDP - 136909
NNPP - 3141
12. Jihar Ekiti
APC- 201,494
LP- 11,397
NNPP - 264
PDP- 89,554
Matata ba za ta koma majalisar dattawa ba, inji Tinubu
Jim kadan bayan da aka sanar ya lashe zabe, Bola Ahmad Tinubu ya yi magana mai daukar hankali.
Zababben shugaban kasan ya ce, ba zai bari matarsa ta koma majalisar dattawa ba, duk da kuwa ta ci zabe kuma ta dade tana aiki a majalisar ta dattawa.
A cewarsa, a madadin zaman majalisa, matar za ta kasance uwar gidan shugaban kasa kuma cikakkiyar mai kula da gida a fadar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng