Bola Tinubu Na Jam'iyyar APC Ya Zama Zababben Shugaban Kasar Najeriya, Shugaban INEC
- Bayan kwanaki uku ana kirga da tattaa kuri'u, an kawo karshen zaben shugaban kasan Najeiya
- Yan takara uku sun fafata matuka inda kowannensu ya samu nasara a jihohi 12 da miliyoyin kuri'u
- Shugaban hukumar INEC ta alanta Bola Ahmed Tinubu, matsayin wanda yayi nasara a zaben
Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasara a zaben shugaban kasar Najeriya 2023.
Asiwaju Tinubu ya samu wannan nasara ne bayan samun mafi rinjanyen kuri'u a zaben jihohi 36 da birnin tarayya Abuja da akayi ranar Asabar, 25 ga Febrairu, 2023.
Tinubu wanda ya lashe zabe a jihohi 12 ya samu jimillar kuri'u 8,794,726 inda wanda ke biye masa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya lashe jihohi 12 da kuri'u 6,984,290 yayinda Peter Obi na jam'iyyar LP ya lashe jihohi 12 da kuri'u 6,101,533.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban hukumar shirya zaben kasa mami zaman kanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana cewa:
"Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC bayan samun kuri'u mafi rinjaye da cika sharuda na doka ya zama zababben shugaban kasar Najeriya."
Ga yadda sakamakon zaben yake:
APC: 8,805,420
LP: 6,101,533
NNPP: 1,496,687
PDP: 6,984,520
Ga Sakamakon jiha-jiha:
Asali: Legit.ng