Gwamnan Benue Ortom Ya Sha Kaye a Zaben Sanata, Dan APC Ya Lashe Zabe
- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya fadi a zaben sanata da aka yi a mazabarsa, inda dan jam'iyyar APC ya lashe
- Jam'iyyar APC ta mamaye kusan dukkan kujerun mazabun majalisun tarayya na jihar a zaben bana
- Gwamna Ortom na daya daga cikin wadanda ke adawa da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sha a kaye a zaben da aka yi sanata a mazabar Benue ta Arewa maso Yamma, dan takarar APC, Chief Titus Zam ya lashe zabe.
Zam ya samu kuri'u 143,151, inda ya lallasa Ortom mai kuri'u 106,882. Dan takarar Labour Party. Mark Gbillah ya samu kuri'u 51,950, The Nation ta ruwaito.
Zam ya fito ne daga karamar hukumar Gwer ta yamma, ya kuma kasance shugaban yankin kana tsohon mai ba gwamna Ortom shawari kan harkar kananan hukumomi da sarautun gargajiya.
Ya kasance jinin siyasar sanata George Akume, ministan ayyuka na musamman da alakar gwamnatoci na Najeriya, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta mamaye Benue a majalisa
Jam'iyyar APC a jihar dai a yanzu ta lashe kujeru 10 cikin 11 na majalisar dokokin kasar nan kamar haka:
1. RT. Hon. Blessing Onu, mazabar Otukpo/ Ohimini
2. Hon. David Ogewu, mazabar Oju/ Obi
3. Hon. Agbese Philip, mazabar Ado/ Okpokwu/ Ogbadibo
4. Chief Mrs Regina Akume, mazabar Gboko/Tarka
5. Arc. Achado Asema, mazabar Gwer/Gwer-west
6. Hon. Sekav Iyortyom, mazabar Buruku
7. Hon. Terseer Ugbor, mazabar Kwande/Ushongo
8. Hon. Prince Solomon Wombo, mazabar Katsina -Ala/Ukum, Logo.
9. Hon Dickson Tarkighir, mazabar Makurdi /Guma.
10. Hon Engr Sesoo GbokoVandeikya/ Konshisha
Bala Na'Allah ya rasa kujerar sanatan da ya dade yana kai
Sanata Bala Ibn Na'Allah ya rasa kujerarsa ta sanata ga wani dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.
Wannan ya faru ne bayan da INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben majalisar dattawa a Kebbi ta Arewa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Ya zuwa yanzu, manyan 'yan siyasa da yawa ne suka rasa kujerunsu a zaben bana, kasancewar zaben ya zo ba yadda aka saba gani ba a kasar.
Asali: Legit.ng