Zaben 2023: EFCC Ta Cafke Yar Shekara 73 Dauke Katin Zabe Masu Dimbin Yawa A Benin
- A ranar Lahadi, kwana daya bayan zabe, 26 ga watan Fabrairu, EFCC ta kama wata dattijuwa da mutane biyu a Benin City, babban birnin jihar Edo
- Jami'an hukumar ta EFCC sun kama matar yar shekara 73 tare da abokan harkallarta ne kan samunsu da katin zabe, PVC, guda 20
- Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anatti ta kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike
Jihar Edo - Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama wata mata yar shekara 73, Comfort Muoneke, dauke da katin zabe, PVC, guda 20.
An kuma kama wasu mutane biyu da ke aiki tare da ita, Afekhana Esther da Segun Osaimokhai.
EFCC ta kamar yar shekara 73 da wasu dauke da PVC guda 20
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar ta EFCC a sanarwar da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta a ranar Lahadi da Legit.ng ta gani ta ce:
"Jami'an hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati na yankin Benin, sun kama mutane uku dauke da katin zabe masu dimbin yawa.
"Daya cikin wadanda ake zargin, Afekhana Esther, an kama ta ne a guduma ta 1, Cocin St. Patrick da ke Ikpoba Okha, Benin City dauke da PVC guda 20 na mutane daban-daban.
"Ta yi ikirarin cewa Comfort Muoneke, wata matar yar shekara 73 da Segun Osaimokhai ne suka ba ta.
"Wadanda ake zargin sun bada bayanai masu amfani kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike."
An cafke wani mutum da miliyoyin naira na sabbi da tsaffin kudi zai kaiwa dan siyasa a Gombe
A bangare guda, kun ji cewa hukumar yaki da rashawa na ICPC ta damke wani Hassan Ahmed da makuden takardun naira da suka hada da sabbi da tsaffi a yayin da mutane ke fama da karancin kudi.
Sojoji na 33 Artillery Brigade dake aikin sintiri a Alkaleri Bauchi ne suka kama mutumin da kudaden cikin jaka da ake yi wa lakabi da 'Ghana must go' sannan suka kai shi wurin ICPC.
Ya amsa cewa an bashi kudin ne domin ya kai wa wani dan siyasa a Gombe daga jihar ta Bauchi.
Asali: Legit.ng