Ni Nafi Cancanta Na Gaji Buhari, Bola Tinubu Ya Fadi Dalilansa
- Dan takarar shugaban kasa a APC ya ce shi ya fi cancanta ya gaji shugaban kasa Muahmmadu Buhari na Najeriya
- Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu, ya bayyana kadan daga cikinsu
- Ya kuma yaba da yadda Buhari ya yi kokarin tsaita kasar da kuma shawo kan matsaloli da yawa da ya samu tun 2015
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ce ya fi sauran ‘yan takarar da ke hamayya dashi.
Tinubu ya bayyana hakan ne ga manema a labarai a wani taron da ya hada a gidansa da ke birnin Legas a ranar Asabar bayan ya kada kuri’arsa, Vanguard ta ruwaito.
A lokuta daban-daban, Tinubu kan bayyanawa ‘yan Najeriya cewa, ya cancanci rike kujerar shugabancin Najeriya saboda dalilai masu karfi da yake bayyanawa.
Na fi sauran ‘yan takarar shugaban kasa, inji Tinubu
A wannan karon ma bata sauya zane ba, ya fito ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Zan iya fada karara cewa na fi sauran ‘yan takara. Ina da wayewa sosai kuma ina da gogewar aiki daga sashen kai da kai.
“Zan yi aiki da wannan kwarewa da gogewa, dama da hange kamar yadda na yi wajen ci gaban jihar Legas.
“Ina da kwarin gwiwar zan ci zaben shugaban kasa.”
Tinubu ya kuma bayyana cewa, yana kokarin ganin ya zama shugaban kasa ne a APC a zaben nan na 2023, rahoton ChannelsTv.
Kalubalen kasa da alkawarin Tinubu
Game da kalubalen da ake fuskanta a kasar, Tinubu ya yi alkawarin warware komai idan aka zabe shi.
A cewarsa:
“Ni mamba ne na jam’iyya mai mulki. Idan na zama shugaban APC, a nan zan sa jam’iyyar ta sake aiki.”
Tinubu ya siffanta shugaba Muhammadu Buhari da jajirtacce kuma shugaba mai gaskiya wanda ya fuskanci tarin kalubale tun farkon hawansa a 2015.
Ya lissafa kadan daga abin da Buhari ya tara da cewa; matsin tattalin arziki, yawaitar adadin jama’a da zaman banza da rashin tsaro.
A jiya Asabar dai an yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, ana ci gaba da tattara sakamako a bangarori daban-daban na kasar.
An samu tashin hankali a wasu bangarori na kasar yayin da ‘yan daba suka sace na’urorin BVAS na tantance masu kada kuri’u.
Asali: Legit.ng