Wasu ’Yan Daba Sun Yi Awon Gaba da Na’urar Aikin Zabe a Katsina da Delta, Inji INEC
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, a yanzu babban abin da 'yan daba suka mai da hankali akai shine na'urar BVAS
- An farmaki rumfunan zabe a jihohin Katsina da Delta a zaben yau Asabar 25 ga watan Faburairu
- A wasu rumfunan a Najeriya, ana ci gaba da kada kuri'u kana babu wani tashin hankali da ake fuskanta
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa, wasu 'yan daba sun yi awon gaba da na'urar tantance masu kada kuri'u ta BVAS da jihohin Katsina da Delta.
Mahmud Yakubu, shugaban INEC ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja kan halin da ake ciki a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.
Yanzu-Yanzu: "Kowane Ɗan Najeriya Zai Kaɗa Kuri'u Idan Ya Yi Abu 1" INEC Ta Yi Jawabi Ana Tsaka da Zabe
Yakubu ya shaida cewa, duba da yadda zaben ke gudana a kasar, alamu sun nuna akwai kalubalen da ba a rasa ba, TheCable ta ruwaito.
Ya ce, kalubalen da ake fuskanta sun hada da matsalar jigilar kayan aikin zaben da kuma rashin tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tuni hukumar ta zabe ta tabbatar da maye gurbin na'urorin da aka sacen don ci gaba da zabe a yankunan.
A ina lamarin ya faru?
A cewar shugaban na INEC, an sace wasu na'urorin ne a karamar Safana ta jihar Katsina a Arewa maso Yammacin Najeriya.
A gefen Kudancin kasar nan kuwa, an sace na'urorin na BVAS ne a karamar hukumar Oshimili ta jihar Delta.
Da yake bayyana matakin da aka dauka, shugaban ya ce an maye gurbin na'urorin yayin da 'yan sanda suka kwato uku daga cikin shida na na'urorin da aka sace a jihar Katsina.
A cewarsa:
"Wannan karon, BVAS ne babban abin harin 'yan daba ba wai akwatunan zabe ba da aka sani a baya."
Ba a tambarin Labour ba a kuri'un jihar Ondo
A wani labarin kuma, kun ji yadda mabiya jam'iyyar Labour suka koka kan rasa ganin tambarin jam'iyyarsu a takardun zabe.
Wannan lamarin ya faru ne a wasu rumfunan zabe na jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Sun bayyana bukatar a soke zaben yankinsu tare da maidashi zuwa wani lokacin da za a sanya sunan jam'iyyarsu.
Asali: Legit.ng