Tashin Hankali, Zaman Makoki Yayin Da Mata Da Miji Da Yaransu 6 Suka Rasu A Gobara A Zaria
- Wani abin tausayi ya faru a unguwar sabon garin Zaria inda wani magidanci da matarsa da yaransu guda shida suka rasu a dare daya sakamakon gobara
- Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faru ne misalin karfe 2 na dare kuma makwabta sun yi kokarin kai musu dauki su kashe wutan amma ba su yi nasarar ceto su ba
- A cewar rahoton, magidancin da abin ya ritsa da shi sunansa Malam Rabiu Mohammed, sunan matarsa Fatima, yaransu kuma kamar haka; Rabiatu, Hauwa'u, Hindatu, Umar, Ibrahim, Abubakar da kuma jinjiri
Zaria, jihar Kaduna - Mazauna unguwar Sabon Gari a Jihar Kaduna, sun shiga zaman makoki bayan gobara ta tashi a wani gida ta halaka mata da miji da yaransu guda shida.
An tattaro cewa gobarar ta fara ne misalin karfe 2 na daren Alhamis yayin da mutanen gidan suna barci, rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce zafin gobarar ne ya tada makwabtansu, wadanda suka fito suka kashe gobarar.
Majiyar, amma, ta ce ba su iya ceto mutanen gidan ba da ransu.
Ya kara da cewa:
"Ba mu ga jami'an kashe gobara ba har sai da dukkan mutanen gidan suka kone."
Sunayen wadanda suka rasu a gobarar
Ya bayyana sunayen wadanda suka rasu kamar haka; Malam Rabiu Mohammed, shine mai gidan da Fatima, matarsa.
Sauran, ya kuma ce yaransu ne su shida, Rabiatu, Hauwa'u, Hindatu, Umar, Ibrahim, Abubakar da kuma jinjiri.
Majiyar ta kara da cewa dukkan kayan da ke cikin gidan ya kone kurmus.
Tuni dai an yi wa mutanen jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.
Ba bu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige, amma ya ce zai bincika ya yi martani.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton kakakin rundunar yan sandan bai yi martanin ba.
Gobara ta yi ajalin wani limami da yaransa biyu da matarsa a Zaria
A baya, an samu rahoton rasuwar wasu iyalan gidan wani mutum mai suna Muhammadu Sani da matarsa Raulatu Sani da dansa Hashim Sani da yarsu Fatima suma sakamakon gobara kuma duk a Zaria.
Hukumar kashe gobara na Zaria ta bakin kwamandanta Muhammadu Umar ta tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda PM News ta rahoto.
Asali: Legit.ng