An Harbi 'Yan Sanda a Tawagar Matar Dan Takarar Majalisa Na PDP a Zamfara
- Labarin da muke samu daga jihar Zamfara ya bayyana cewa, an farmaki tawagar matar dan takarar majalisa
- An harbi 'yan sanda biyu tare da raunata wasu mutane daban da ke tare da matar a lokacin da take dawowa Gusau
- Ana ci gaba da samun hare-hare tun lokacin da zaben shugaban kasa ya karato a Najeriya ta kowane bangaren kasar
Jihar Zamfara - An harbi wasu jami'an 'yan sanda da ke a tawagar matar dan takarar majalisa a PDP, Hurriyah Lawal a wani rikici da ya barke tsakanin tawagar da rundunar yaki da 'yan daba ta jihar Zamfara.
Wannan lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar ranar Juma'a a lokacin da Mrs Hurriyah ke dawowa Gusau daga wata tafiya.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Imran Ahmad, mai magana da yawun matar dan takarar ya ce jami'an sun gamu da tsautsayin ne a farmakin da rundunar ta kawo musu.
Martanin rundunar yaki da 'yan daba
Sai dai, Bello Bakyasuwa, shugaban rundunar yaki dan 'yan daba ta Zamfara ya magantu, ya ce jami'ansa na kan aiki ne a lokacin da suka gamu da 'yan bangan siyasa da safe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Tabbas, an farmaki jami'anmu da sanyin safiyar ranar Juma'a, suna kan aikin sintiri sai wasu 'yan daba da ke ihun "karya ne" suka tare su suka fara harbi kan rundunar yaki da 'yan daba, ba mu da zabin da ya wuce mu rama."
Bakyasuwa ya kuma bayyana cewa, an kama wasu 'yan daba biyu da har yanzu suna hannun hukuma, rahoton Punch.
Da aka tambaye shi game da raunata 'yan sanda, ya ce bai da masaniya a kai tukuna.
Sai dai, rundunar 'yan sanda ta ce za ta fitar da rahoto game da lamarin a lokacin da aka tuntube ta don jin gaskiyar abin da ya faru.
Yadda aka dasa bam a gidan dan takarar majalisa na APC a Ribas
A wani labarin kuma, an farmaki gidan wani dan takarar majalisa a jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya.
Wannan harin na zuwa ne a jajiberin zaben shugaban kasa da za a yi a gobe Asabar 25 ga watan Faburairu.
Asali: Legit.ng