Shugabar Karamar Hukuma Ta Rasu Bayan Halartar Wani Taro Kan Zaben Shugaban Kasa
- Yanzu muke samun labarin yadda wata shugabar karamar hukuma a jihar Ribas ta kwanta dama ana saura kwana daya zabe
- An ce Mrs Esther Bassey ta halarci tarukan siyasa a jihar kafin ta kwanta bacci, daga baya tace ga garinku nan
- Ana ci gaba da shirin zaben 2023 na shugaban kasa, an samu asarar rayuka da yawa kafin a kada kuri'a gobe Asabar 25 ga watan Faburairu
Jihar Ribas - Allah ya yiwa shugabar karamar hukumar Calabar ta Kudu a jihar Ribas, Mrs Esther Bassey.
Majiya ta bayyana cewa, Mrs Bassey ta rasu ne bayan halartar wani taron tattaunawa kan tafiyar da zaben bana da aka gudanar, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake martani game da lamarin, daya daga cikin hadimar marigayar ta ce, shugabar ta kasance lafiya kalau a daren jiya.
A cewar hadimar:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ta halarci wasu taruka na shirin zaben shugaban kasa na gobe. Ta halarci wani taron a jiya da dare.
“Bata nuna alamar gajiya ko rashin lafiya ba lokacin da ta gama da yamma.”
Tsohuwar shugabarm karamar hukumar an ce ta rasu ne da dare da misalin karfe na 4am a birnin Calabar, rahoton Vanguard.
Marigayiyar ta kasance mamba a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
'Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake a Jihar Imo, Sun Kone Gidajen Shugabannin APC da LP
A bangare guda, an sace wata matar basaraken jihar Imo tare da kone gidajen shugabannin jam'iyyun siyasa na APC da LP a wata gunduma ta jihar.
Wannan al'amari ya tada hankali, mazauna da yawa a yankin Amuro na karamar hukumar Okigwe sun shiga tashin hankali, wasu sun tsere daga cikin gidajensu.
Yanzu-Yanzu: Hoto, Bayanai Sun Fito Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Sanannen Dan Majalisar Wakilai Da Dala 498,000 Cikin Jaka
Karamar hukumar Okigwe na daga cikin kananan hukumomin da ake yawan samun hare-haren 'yan ta'adda a cikin wadannan shekarun.
'Yan daba sun kone motoci shida, an kama tsageru 55 a Kano
A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu 'yan daba suka mamaye gangamin kamfen dan takarar shugaban kasa an NNPP.
Wannan lamari ya kai ga kone motoci guda shida tare da raunata magoya bayan Rabiu mUSA Kwankwaso.
A bangaren jami'an tsaro, an kama 'yan daba 55 da ake zargin suna da hannu a aika-aikan da aka yi a jihar.
Asali: Legit.ng