An Garƙame iyakokin Najeriya, Domin Gudanar da Babban Zaɓen Ƙasa.
- Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya Ya Hori Jami'an Sa Dasu Tabbatar Da Sun Zartar Da Dokar Nan Take
- Yace Dokar Idan An Zartar Zata Hana Duk Wani Mahaluki Shiga Ko Fita Daga Ƙasar
- A Cewar Kwanturola Janar din, an Ɗauki Matakin ne Domin Tabbatar Da Babu Wani Tasgaro Da Zai Shigo Daga Waje Da Zai Iya Shafar Sahihancin Zaben
Abuja - A yayin da ake jaji-barin gudanar da babban zaɓen ƙasar nan, gwamnatoci daga ko wanne ɓangaren na cigaba da ɗaukar matakai domin ganin an samu sahihin zaɓe ba tare da wani ƙorafi daga masu saka ido na ciki dana waje ba.
Ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka ya haɗa da canja fasalin kuɗi tare da rage yawan kuɗaɗen da suke yawo a hannun jama'a a wani salo na rage tasirin siyan ƙuri'u a hannu talaka mai neman na kaiwa bakin salati.
Ana tsaka da wannan dambarwa ne sai gashi gwamnatin Najeriya har ila yau ta sanar da shirin ta na garƙame duk wata iyaka da take dashi a cikin iyakokin ƙasar ta a gobe asabar idan Allah ya kaimu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kullewar ta haɗa da duk wata iyaka da kasar take dashi musamman ma iyakar ruwa, data ƙasa kamar yadda Isah Idris wanda shine Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ya tabbatarwa masu neman labarai a ranar Alhamis ɗin data gabata.
A cewar sa:
"Gwamnatin tarayya tana umartar zaratan jami'an mu dasu tabbatar da sun kulle duk wata hanyar shige da fice ta ƙasa tun daga daren yau na ƙarfe goma sha biyu 25 ga wata, 2023 zuwa 12 na ranar Lahadin 26ga watan Fabrairu, 2023." Inji Shi.
Hakan kamar yadda Idris ya shaidawa Arise News, wani mataki ne da aka ɗauka domin a tabbatar da anyi gamida ƙarƙare zaɓen cikin tsari tare da samun abinda ake so.
"Duk wasu shugabannin shiyya shiyya na ɓanagren iyakar ƙasa, muna umartar su domin tabbatar da an bi dokar nan sau da ƙafa."
Gobe dai rana ce mai muhimmanci da ƴan Najeriya zasu zaɓi masu jagorantar ƙasar domin Shugabancin ta zuwa shekaru masu zuwa, wanda ya haɗa da ƴan Majalisar Tarayya da Kuma Sanatoci.
Yan takara sun yi alkawarin zaman lafiya
A wani labari mai kamanceceniya da wannan kuwa, jiga-jigan yan takarkarun Shugabancin Najeriya tuni suka rattaba hannun yarjejejiniya domin tabbatar da zaman lafiya yayin da kuma bayan an gudanar da zaben na gobe.
Daga cikin wadanda suka halarci taron da aka yi a ranar Laraba a Abuja akwai Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na jam'iyyar APC da takwararsa Alhaji Atiku Abubakar na APC.
Asali: Legit.ng