Buhari Ya Sauka Daura, Jihar Katsina Domin Kada Kuri’arsa a Zaben 2023

Buhari Ya Sauka Daura, Jihar Katsina Domin Kada Kuri’arsa a Zaben 2023

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta isa Daura domin sauke hakkin dimokradiyya a zaben bana da ke rafe ranar Asabar
  • Buhari ya samu tarbar jiga-jigan siyasar jihar Katsina, ciki har da gwamna da wasu kwamishinoni
  • Ana kyautata zaton Buhari zai kada kuri’arsa ne a gundumar Sarkin Yara (A) da ke cikin kwaryar Daura a jihar da ke Arewa maso Yamma

Jihar Katsina - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 23 Faburairu, 2023 ya isa Daura, garinsu a jihar Katsina domin kada kuri’arsa a zaben 2023 na shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.

Shugaban kasan ya sauka ne a filin jirgin Umaru Musa Yar’adua da misalin karfe 4:41 na yamma, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Buhari kan yi zabe ne a rumfarsa da ke Sarkin Yara (A) a Daura ta jihar Katsina, a wannan karon ma ya zo don kada kuri’ar dimokradiyya.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC Jahili ne: Cewar Gwamnatin Kogi Bayan Kotu Ta Kwace Wasu Kadarorin Gwamnanta

Buhari ta isa Daura don kada kuri'arsa
Buhari tare da jama'ar Daura | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna ya tarbi Buhari da mukarrabansa

Buhari ya samu tarbar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da sauran mambobi da kusoshin gidan gwamnatin jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga cikin manyan gwamnatin Katsina da suka karbi Buhari sun hada da alkalin alkalan jihar, mai shari’a Musa Danladi Abubakar, kwamishinan lafiya, Eng. Yakubu Nuhu Danja da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a jihar.

‘Yan siyasa, ‘yan kasuwa da sauran manyan ma’aikatan gwamnati duk sun hallara domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

A ina Buhari zai kada kuri’arsa?

Ana sa ran Buhari zai kada kuri’arsa a ranar Asabar a gundumar Sarkin Yara (A) mai rumfunan zabe 15 a karamar hukumar Daura ta jihar.

A wannan zaben ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai cika shekaru takwas a kan mulkin Najeriya, za a yi zabe ne domin samo wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

Saura kiris zabe: Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka dasa bam a gidan TV da rediyo a jihar Ribas

An fara rabon muhimman kayayyakin aikin zaben 2023

A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kanta ta fara rarraba kayayyakin da za a yi aikin zabe dasu a ranar Asabar mai zuwa.

A jihar Gombe, hukumar tuni ta fito da kayayyakin daga wani dakin ajiya da ke cikin Babban Bankin Najeriya (CBN) da a jihar.

Ya zuwa yanzu, hukumar ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaben a ranar Asabar 25 ga watan Faburairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.