Za’a Yi Amfani da Karfi Soja Kan Wadanda Ke Shirin Kawo Tsaiko Ga Zaben Ranar Asabar, Inji Rundunar Soji

Za’a Yi Amfani da Karfi Soja Kan Wadanda Ke Shirin Kawo Tsaiko Ga Zaben Ranar Asabar, Inji Rundunar Soji

  • Yayin da ake ci gaba da fuskantar zaben 2023 mai zuwa a ranar Asabar, hukumar tsaron Najeriya ta yi magana
  • Rundunar sojin Najeriya ta ce, za ta yi amfani da karfin ikonta wajen tankwara masu kawo tsaiko ga zaben na bana
  • A baya INEC da hukumomin tsaro sun ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaben bana cikin tsanaki

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, za ta yi amfani da karfin iko kan duk wani wanda ya kawo tsaiko ko ya yi kokarin lalata faruwar zaben ranar Asabar mai zuwa.

Wannan na fitowa ne daga bakin mukaddashin daraktan yada labarai na rundunar. Brig.-Gen. Tukur Gusau a ranar Alhamis 23 Faburairu, 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a hedkwatar tsaro ta Najeriya a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da yanayin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC Jahili ne: Cewar Gwamnatin Kogi Bayan Kotu Ta Kwace Wasu Kadarorin Gwamnanta

Soja za dauki mataki kan masu kawo tsaiko a zabe
Zaman da aka yi nkan lamarin tsaro | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daga cikin wadanda suka halarci wannan zaman akwai kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar sojin sama, AC Wap Maigida da dai sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a yi zabe ba tare da matsala ba, inji hukumar tsaro

Idan baku manta ba, hafsoshin tsaron Najeriya sun tabbatarwa shugaba Buhari cewa, za a yi zaben 2023 cikin tsanaki kamar yadda aka tsara.

Sun fadi hakan ne a ranar Laraba lokacin da suka gana da shugaban kasan kan yadda zaben bana zai kasance.

Majalisar koli kan harkar tsoro a Najeriya ce ta hada ganawar da Buhari, kuma tawagar ta hada shugabannin hafsun soji, IG na ‘yan sanda, wasu ministoci da dai sauran masu ruwa da tsaki.

A tun farko, hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatarwa ‘yan najeriya cewa, za a yi zaben 2023 cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: An kai muhimman kayan aikin zabe shugaban kasa jihar Gombe, INEC ta magantu

A bangare guda, rundunar sojin ta sake layukan da za akira don kai rahoton masu kawo tsaiko ga zabe, rahoton PM News.

Motocin jigilar kayan aikin zabe sun makale a jihar Kuros Riba

A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu manyan motocin da suka dauko kayan aikin zabe suka makale a wani yankin jihar Kuros Riba.

A yanayi irin wannan, lamarin ya dauki hankalin jama’a a kafar sada zumunta, musamman Twitter.

Wannan na zuwa ne yayin da ya saura kwanaki biyu kacal a yi zaben 2023 na shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.