'Yan Daba Sun Kone Motoci, Sun Tara Hanya Yayin da Kwankwaso Ke Gangamin Kamfen a Kano

'Yan Daba Sun Kone Motoci, Sun Tara Hanya Yayin da Kwankwaso Ke Gangamin Kamfen a Kano

  • Wasu ‘yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso a wani yankin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Wannan lamari ya haifar da hargitsi, domin an kone motoci da kayayyaki masu amfani a mummunan farmakin
  • Ya zuwa yanzu, an girke jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don ba da tsaro a inda abin ya faru

Jihar Kano - Wasu tsagerun ‘yan daban da ba a san ko su waye ba sun farmaki ayarin motocin tawagar gangamin jam’iyyar NNPP a kusa titin Na’ibawa zuwa Zaria a jihar Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mabiya bayan NNPP da ke cikin motocin suna kan hanyarsu ne ta zuwa Kwanar Dangora domin tarbar dan takarar shugaban kasan jam’iyyar, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Zai Dura Kano Domin Yin Yawon Kamfen Karshe a Yakin Zaben 2023

Kwankwaso ya zo jihar Kano ne domin yin gangamin kamfen na karshe na takarar shugaban kasa da yake yi a jihar Kano.

An farmaki 'yan a mutun Kwankwaso a Kano
Yadda aka yiwa 'yan a mutun Kwankwaso barna a Kano | Hotuna: dailytrust.com
Asali: UGC

Akalla, motoci 10 ne aka farmaka yayin da aka kone wasu motocin da yawa a wannan mummunan farmaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne awanni kasa da 24 bayan da dukkan jam’iyyun siyasa suka da ‘yan takararsu suka sanya hannu kan yajejeniyar zaman lafiya a birnin tarayya Abuja.

Shaidan gani da ido ya magantu

Wani ganau da ya sha dakyar a lokacin farmakim Tasiu Lawal ya bayyana cewa, ya tsere ne ya bayan motar da yake ciki.

Ya ce:

“Dakyar na sha. Alhamdulillah. An fada mana cewa (‘yan daban) suna can suna jiranmu, son haka, sai muka jira a Na’ibawa don mu tabbatar muna da yawa kafin mu wuce.
“An yi rashin sa’a, sai suka zo ta ko’ina suka farmake mu. Nan take suka fara farmakarmu, har da mata, da adduna.”

Kara karanta wannan

Saura kiris zabe: Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka dasa bam a gidan TV da rediyo a jihar Ribas

Ya zuwa yanzu dai an girke jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ‘yan sanda, jami’an NSCDC da dai sauransu a wurin da lamarin ya faru.

An kone gidajen shugabannin APC da LP a jihar Imo

A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu tsagerun ‘yan ta’adda suka farmaki gidajen wasu ‘yan siyasa a jihar Imo.

Hakazalila, rahoton ya bayyana cewa, an yi awon gaba da matar wani basaraken yankin, lamarin da ya kawo cece-kuce.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.