Sojoji Sun Cafke Ɗaya Daga Cikin Waɗanda Suka Shirya Harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasarar cafke wasu miyagun ƴan ta'adda a jihar Kaduna
- Ɗaya daga cikin miyagun ƴan ta'addan da aka cafke na daga cikin waɗanda suka shirya harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna
- Sojojin sun kuma ƙwato wasu muhimman kayayyaki a hannun ƴan ta'addan da suka shigo hannu
Abuja- Hedikwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta sanar da cewa dakarun sojoji sun cafke wasu ƴan ta'adda a ƙauyen Damba, cikin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
A cewar hukumar, ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da aka kama ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka kitsa harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna na ranar 28 ga watan Maris, 2022. Rahoton Punch
Darektan watsa labarai na hukumar, Manjo Janar Musa Danmadami, shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa.
Sanarwar hukumar tsaron na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Dakarun sojoji na atisayen Whirl Punch, a ranar 14 ga watan Fabrairun 2023, sun kai sumame bayan samun rahoton ɓullar wasu manyan ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP a ƙauyen Damba cikin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna."
"Sojojin sun garzaya wurin sannan suka cafke ƴan ta'adda guda uku. Ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da aka cafke, yana daga cikin waɗanda suka kitsa kai harin ta'addanci kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022."
“Bayan kai sumamen, sojojin sun kwato babura guda biyu, wayoyin hannu guda biyu da tsabar kuɗi har dala dubu biyar ($5,000) da wasu irin kuɗaɗen da sauran kayayyaki."
Yan Bindiga Sun Sace Matar Basarake a Jihar Imo, Sun Kone Gidajen Shugabannin APC da LP
A wani labarin na daban kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a wata jiha a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya, ana dab da a fara babban zaɓen 2023.
Ƴan bindigan a yayin harin sun sace matar basaraken Amuro na karamar hukumar Okigwe a jihar Imo, Uzoeze Umugborogu.
Bayan miyagun ƴan bindigan sun sace matar basaraken, sun kuma kai sumame gidajen shugabannin jam’iyyun APC da LP na gundumar Amuro, inda suka banka musu wuta.
Asali: Legit.ng