Wani Dan Ya Fito da Tsabar Kudi da Ya Tara Tsawon Shekaru 10, Ya Siya iPhone X da Su

Wani Dan Ya Fito da Tsabar Kudi da Ya Tara Tsawon Shekaru 10, Ya Siya iPhone X da Su

  • Wani dan Najeriya ya sha ajiya yayin da ya tara kudadensa na tsawon shekaru 10, ya fito dasu don siyan waya iPhone
  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da mutumin ya fitar da takardar shaidar siyan waya da makudan kudaden a kusa dashi
  • A bidiyon an ce, mutum ya shafe shekaru 10 ne yana ajiye N100, sai kawai ya fito dasu lokacin da ake cikin karancin Naira

Wani dan Najeriya ya yi amfani da kudin da ya tara tsawon shekaru 10 ya siya waya kirar iPhone don shima a dama dashi.

A bidiyon da aka yada a shafin @mrcake007 na TikTok, an ga mutumin matashi a shagon siyar da waya, inda ya ce da kudinsa don siyan iPhone.

Matashi ya tara kudi ya siya iPhone
Hotunan matashin da ya siya iPhone da kudin da ya tara cikin shekaru 10 | Hotuna: TikTok/@mrcake007 and Oscar Wong/Getty Images.
Asali: UGC

Da ajiyarsa ta shekaru 10 ya siya iPhone X

A bidiyon, an ce mutumin ya tara ‘yan N100 na tsawon shekaru, inda yanzu kuma ya yanke shawarin amfani da kudin don siyan waya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Sarki Sanusi ya tona asirin abin da aka kitsa wajen sauya fasalin Naira

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma ga lokacin da ya isa shagon da tulin kudi, akalla dami takwas duk na ‘yan N100 ko a jikinsa.

Duk da cewa ba a san adadin kudin ba, wasu ‘yan TikTol sun yi ta luguden lebe cewa, kudin sun fi karfin kudin waya kirar iPhone C guda daya.

Koma dai ya ne, an ga mutumin na sanya hannun kan rasitin siyan wayar a cikin bidiyon da ya yi shuhura a kafar sada zumunta.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar TikTok

@Olisa:

"Kenan kai ka kawo karancin Naira 100 a Najeriya.”

@Nwonueze:

"Shi da zai dauka ya buga wasan caca dango biyu.”

@David:

"Ya zaka yi idan wayar ta fashe bayan ka siya.”

@Favorite celebrity:

"Duk wannan kudin don siyan X? Naira bata da daraja.”

@Danny Snoop:

Kara karanta wannan

Mu na Shan Wahala: Ranar Nan Rashin Kudi Ya Jawo Mun Gaza Dafa Abinci - Sanata

"Abin da banki ya bashi ne kada ka kula duk wadannan.”

@Ndubuisi Emmanuel:

"Ka adana ‘yan Naira 100 na shekaru 10 kuma ka zo ka siya iPhone da kudin, Ina gobe take ga wannan abu.”

Wani matashin kuma, kirkirar takalma ya yi masu ban mamaki, inda aka gansu sak takalmi sau ciki da kowa zai iya sakawa.

An ga bidiyon takalma sau ciki na karfe da wani fasihi ya kera, sai dai wa zai iya sakawa?

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.