Wasu Kasurguman ’Yan Bindiga Sun Farmaki Gidan Talabijin da Rediyo a Jihar Ribas
- Wasu gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan gidan talabijin da rediyo a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya
- Wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 21 ga watan Faburairun 2023 yayin da ake shirin babban zaben kasar
- Ba wannan ne karon farko da ‘yan ta’adda ke kai farmaki kan wuraren ayyukan halas da na gwamnati ba a yankin Kudu
Jihar Ribas - Wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan wani gidan talabijin a birnin Fatakwal na jihar Ribas da ke kudancin Najeriya, rahoton Channels Tv.
Rahoton da muke samu daga gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, an farmaki gidan yada labaran Atlantic Tv da Wish 99.5 FM da ke Ozuoba da nakiya.
A cewar rahoton, lamarin ya faru ne da bisalin karfe 8:45 na daren ranar Talata, 21 ga watan Faburairu.
Mai gidan yada labarai ya magantu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga majiya, mai gidan yada labaran, Chinyere Igwe, wanda kuma dan majalisar wakilai ne ya ce an lalata dakin janareta a harin.
A cewarsa:
“Mun sanar da ‘yan sanda, wani sashe na ‘yan sanda ya zo kuma DPO ya kira ni a yau ya ce wasu kwararru kan ilimin nakiya za su zo su fadada bincike.”
Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda bata yi martani kan lamarin ba, domin kuwa ba samu jin ta bakin kakakin rundunar jihar ba, Grace Iringe-Koko, rahoton Leadership.
Ya zuwa yanzu dai, an yi nasara ba a samu rasa rai a harin ba, hakazalika babu wani wanda ya samu rauni daga cikin wadanda ke cikin gidan yada labaran.
Ana yawan samun hare-haren ‘yan ta’adda a yankunan Kudancin kasar nan, musamman daga ‘yan awaren IPOB.
‘Yan bindiga sun farmaki ofishin ‘yan sanda a Anambra
A wani labarin kuma, kun ji yadda ‘yan sanda suka hallaka wasu ‘yan bindiga a wani harin da suka kai a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla ‘yan bindiga uku ne suka mutu, kuma an kwato makamai da kayan aikata laifi.
A gefe guda, an hallaka wasu jami’ain ‘yan sanda da ke kan aiki a lokacin da tsagerun suka tsara kone ofishin yanki na ‘yan sanda.
Asali: Legit.ng