Tsohon Shugaban APC Ya Raba Gari da Shugaba Buhari Kan Sauya Naira
- Tsohon gwamnan Edo, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya nuna adawa da sabon tsarin CBN na sauya fasalin naira
- Oshiomhole, tsohon shugaban APC ya nesanta kansa da matakin shugaban kasa Buhari na saɓa wa umarnin Kotu
- Ana ta kace-nace musamman a jam'iyyar APC mai mulki tun bayan bullo da shirin sauya fasalin N200, N500 da N1000
Edo - Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana rashin gamsuwa da matakin shugaban ƙasa, Muhammadi Buhari, kan sauya fasalin naira.
Oshiomhole, wanda ya yi jawabi a cikin yaren Pidgin a wata Kasuwa da ke Auchi, jihar Edo, ya nesanta kansa daga kalaman baya-bayan nan da shugaban kasa ya yi kan sabon tsarin.
Ya kuma roƙi mai girma shugaban kasa ya girmama umarnin Kotun koli kan batun kana ya soki tsarin sauya naira baki ɗaya a daidai lokacin da ake kakar zaɓe.
A rahoton Tribune, Kwamaret Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duk wannan wahalar da Buhari ya jefa mutane bani da hannu a ciki, jam'iyyar mu ta faɗa wa shugaba Buhari cewa bai kamata ya sauya takardun kuɗi a lokacin zaɓe ba."
"Duk abinda ka gaza yi a tsawon lokacin da ka share kan mulki, bai kamata ka zo da shi don ruguza tsarin wani ba, ko kaɗan ba abu ne mai kyau ba."
Bugu da ƙari, tsohon gwamnan ya roki shugaban kasa Buhari ya yi biyayya ga umarnin Kotun koli, wanda a cewarsa yana sama da duk wani matakin shugaban ƙasa.
Game da batun sabbin naira kuma Mista Oshiomhole ya ce bai kamata yan Najeriya su watsar da tsoffin kuɗinsu ba domin suna da ƙima da halasci inji Kotun ƙoli.
A cewarsa, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, sauka zai yi bayan zabe amma kudin da mutane zasu ci gaba da amfani suna nan, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.
"Zuwa lokacin da kuka gama kaɗa kuri'unku ranar Asabar, gwamnan CBN ya gama lokacinsa, kuɗinku na nan amma shi kansa shugaban ƙasa zai ƙare."
CBN Ya Fara Rabawa Mutane Takardun Sabon Naira Gida-Gida a Kano
A wani labarin kuma babban banki ya bullo da sabon shirin tura wakilai gida gida a jihar Kano domin ragewa mutane wahala.
A cewar ɗaya daga cikin wakilan da babban bankin ya tura, wannan tsarin zai taimaka matuka gaya wajen rage wa Kanawa wahala.
Asali: Legit.ng