‘Kada Ka Bari Tartsatsin Wuta Ya Taba Su’: Jama'a Sun Shiga Mamaki Bayan Ganin Kyakkyawan Takalmin Karfe

‘Kada Ka Bari Tartsatsin Wuta Ya Taba Su’: Jama'a Sun Shiga Mamaki Bayan Ganin Kyakkyawan Takalmin Karfe

  • A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga takalim da aka yi da karfe ya jawo cece-kuce
  • A bidiyon da ya yi shuhura a shafin TikTok na @minimumio, mutane sun kadu bayan ganin takalmin a ajiye
  • Akalla mutane miliyan 8 ne suka kalli bidiyon, kuma ya ba mutane dariya matuka, sai wanda ya gani

Ba sabon abu bane ganin abubuwa banbarakwai a duniyar kwalliya, bidiyon takalmin karfe na daga cikin irin wadannan misalai.

Wani dan TikTok, @minimumio ya bar jama'a baki bude lokacin da ya yada bidiyo mai ban dariya na wasu takalman karfe masu daukar hankali.

Takalman da aka buga da hannu sun bayyana karara an yi su ne da bakin karfe, kuma ga su nan sau ciki ne har da igiyarsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wani Mutum Dan Tsurut Da Ya Halarci Gangamin Kamfen Din Tinubu Cikin Salo Ya Ja Hankali

Yadda takalmin karfe ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta
Takalmin karfen da ya jawo cece-kuce a TikTok kenan Hoto: @minimumio (TikTok)
Asali: UGC

Kalli bidiyon:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Martanin jama'ar TikTok

Bayan ganin bidiyon a kafar ta sada zumunta, jama'a sun yi martani, sun bayyana abin d ake ransu game da wannan ta

user8371272840974:

"Lallai zubin ya dace dan adam."

mutskan23:

"Wannan takalmin kariya ne mai kyau."

user6395853300250:

"Ana amfani dasu ne wajen ba 'yan bindiga da 'yan Boko Haram horo."

glenroybaker653:

"Kada ka bari tartsatsin wuta ya taba su kana sanye dasu."

LX:

"Wadannan su ne Airforce One bugun 2023."

Clibo Van Savage:

"Sun yi amfani da wadannan takalman a Mad Max."

user1965518861739:

"Za ka yi amfani da wadannan takalman har karshen rayuwarka."

Thabo:

"Ina bukatarsu ga wani gani ba." Wancan yaron matsala ne."

Love Lock:

"Ta yaya kafafunka za su zauna cikin salama a ciki... zai kumbura kafa."

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje Yace China Ta Kawo COVID-19, CBN Ya Kawo COVID-23

Muktar Wadhanole:

"Kuma wani zai yi amfani dasu a haka."

Bidiyon yadda wani ya yiwa wani yaro aski da cokali

A wani labarin na daban, wani matashi ya ba da mamaki yayin da aka ga yana cancara aski ga wani yaro da cokalin cin abinci.

Wannan lamarin dai ya ja hankalin mutanen kafar sada zumunta, wasu suna ganin ba zai yiwu a yiwa dan adam askin gashin kai da cokali ba.

A bangare guda, wasu sun bayyana gano hanyar da ya yi na yin askin, amma sun ce tabbas ba da cokali ya yi, Allah ne masani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.