Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC, Bola Tinubu Ya Dura Legas Don Halartar Wani Muhimmin Taro
- Dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ya gana da shugabannin Yarbawa da na yankin Kudu maso Yamma gabanin zabe
- An ce Tinubu ya dura jihar Legas ne domin halartar wannan ganawa a ranar Litinin 20 ga watan Faburairun wannan shekarar
- 'Yan siyasa da jam'iyyunsu na ci gaba da kira ga kowa da ya fito a yi zaben 2023 dashi don kawo shugaba ba gari
Jihar Legas – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya dura jihar Legas a ranar Litinin 20 Faburairu, 2023.
A cewar Jubril Gawar, wani hadimin gwamna Babajide Sanwo-Olu, Tinubu ya dura ne a otal Eko don halartar wani taron Yarbawa da shugabannin yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.
Sanarwar da Gawat ya fitar ta ce:
“Shugaban kasan Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya iso otal dn Eko don ganaawa da shugabannin Yarbawa da na Kudu maso Yamma.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ku dage ku zabi Tinubu: Shawarin APC ga 'yan Najeriya baki daya a zaben bana
A bangare guda, jam'iyyar APC ta bayyana bukatar 'yan Najeriya su maida hankali tare da ba Tinubu kuri'unsu a zaben 2023 da ke tafe nan kusa.
Jam'iyyar ta bayyana cewa, Tinubu ne zai kawo karshen duk wani yanayi da kasar ke ciki tare da warware komai yadda ya kamata.
Hakazalika, jam'iyyar ta ce Tinubu zai daidaita lamarin da ke alaka da sauyin kudi da kuma karanin sabbin Naira da ake fuskanta a halin yanzu.
A bangaren an fetur da matsayin tattalin arziki, duk dai jam'iyyar ta ce amsan shine a ba Tinubu a ga kamun ludayinsa a zaben na bana.
'Yan siyasa ne za su fi damuwa da batun sauyin kudi, inji Sarki Sanusi
A wani labarin kuma, tsohon sarkin Kano Sanusi ya bayyana gaskiyar abin da ke tattare da sauya kudin kasar nan da aka yi a watan Disamban bara.
Sanusi ya ce kada 'yan Najeriya su daga hankalil hakan ba zai cutar dasy kamar yadda ya cutar da 'yan siyasa mahandama ba.
Ya kuma bayyana cewa, Najeriya dama ta shirya karbar wannan sauyi na kudi, kuma kowa zai ga fa'idarsa.
Asali: Legit.ng