Tashin Hankali Yayin da Wata Sabuwar Girgizar Kasa Ta Afkuwa a Kan Iyakar Kasashen Turkiyya da Siriya
- An sake samun wata mummunar girgizar kasa a kasashen Siriya da Turkiyya da yammacin Litinin 20 Faburairu, 2023
- An ruwaito cewa, an samu raunuka masu yawa, kuma girgizar na zuwa ne makwanni biyu bayan faruwar ta farko da ta kashe mutane sama da 40,000
- Ba wannan ne karon farko da aka fara samun girgizar kasa a wasu kasashen waje ba, hakan ya sha faruwa a lokuta daban-daban
Siriya - An sake samun wata sabuwar girgizar kasa da ta auku a iyakar kasashen Turkiyya da Siriya, kwanaki bayan afkuwar ta faro da mutane sama da 40,000 suka kwanta dama a kasashen biyu.
A cewar kamfanin dillacin labaran Sriya na SANA, girgizar kasar mai girman 6.4 ta daki yankin Hatau ne na kasar Turkiyya, wacce ta yi barna a makwanni biyu da suka gabata.
Tashin Hankali: Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa
Har ila ya, a yankin Siriya, akalla mutane shida ne suka mutu a Aleppo daga baraguzan gini yayin da a kasar Turkiyya kuwa, gine-gine masu yawa suka ruguje tare da danne dubban mutane.
Duk da cewa babu wasu rahotanni da ke bayyana rasa a rai a sabuwar girgizar, amma wata kafar yada labarai ta Turkiyya, Anadolu ta ce, girgizar ta shafi kasashen Siriya, Jordan, Isra’ila da Masar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yanayi ya sauya bayan samun girgiza ta biyu
An ruwaito cewa, mutanen da lamarin ya faru a yankinsu sun rasa wutar lantarki da sabis na yanar gizo, kuma mutane da yawa ne suka fice daga gidajensu zuwa budaddun wurare don gudun rugujewa gine-gine.
Hukumomin kasar Siriya sun ankatar da ‘yan kasar da su bi ka’idojin da gwamnati ta gindiya tun faruwar girgizar kasar farko tare da ba da hadin kai wajen ceto wadanda gine-gine suka danne.
A wani rubutu na Twitter, hukumar tsaron farin kaya ta kasar Siriya ta ce, jami’anta na can suna kokarin aikin ceto a ankin da lamarin ya faru.
Yadda lamarin ya faru da halin da ake ciki a yanzu
A cewar rubutun:
“Birane da garuruwa masu yawa a Arewa maso Yammacin Siriya sun gamu da bugun girgizar kasa har sau biyu da ya faru a Kudancin Turkiyya da yamman nan, Litinin 20 Faburairu.
“Dalilin haka, katangu da zaurukan gidaje da yawa sun ruguje a yankunan. Jami’anmu na kokarin yiwa wadanda suka samu raunuka jinya a yankunan.
“Fararen hula da yawa sun samu raunuka daga baraguzan gini, turmutsusu da tsalle daga wurare masu tsawo. Bugu da kari, a yankin Jenderes, Arewacin Aleppo wani ginin da babu mutane a cikinsa da husumiya sun ruguje.”
A baya mun kawo uku rahoton yadda girgizar kasar ta hallaka mutane sama da 44,000 nan take a kasashen biyu.
Asali: Legit.ng