Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke Kan Ƙarancin Kuɗi a Jihar Ogun

Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke Kan Ƙarancin Kuɗi a Jihar Ogun

  • Sabuwar zanga-zanga ta sake ɓarkewa a jihar Ogun kan ƙarancin kuɗin da ake fama da shi
  • Ko a makon da ya gabata sai da aka samu zanga-zanga a jihar inda mutane suka toshe wata babbar hanya
  • A sabuwar zanga-zangar da ta ɓarke yau, an cinnawa wasu muhimman bankuna wuta

Zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Ogun kan ƙarancin kuɗi. Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a yanar gizo sun nuna bankuna biyu na ci da wuta a yankin Sagamu na jihar.

Bidiyiyon da aka yaɗa a ranar Litinin, sun nuna mutane na kallo yayin da bankunan Keystone da Union ke ci da wuta yayin da wasu matasa ne ɗauke da alluna suna zanga-zanga. Rahoton The Punch

Sabbin kudi
Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke Kan Ƙarancin Kuɗi a Jihar Ogun
Asali: Facebook

A ranar Juma'a a makon da ya wuce, an samu zanga-zanga a ƙaramar hukumar Mowe-Ibafo ta jihar Ogun, inda mutane da dama suka toshe hanyar Legas zuwa Ibadan, domin nuna ɓacin ran su kan wahalar da ƙarancin kuɗi ya janyo a ƙasar nan

Kara karanta wannan

Zanga-Zangar Karancin Sabbin Kuɗi Na Zama Barazana ga Zaɓe? INEC Ta Sake Magana Kan Yuwuwar Zaɓen 2023

Da suke magana kan lamarin da ya auku a shafin Twitter, wasu mutane sun yi ƙarin haske kan abinda ya auku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@arranowanna ya rubuta cewa,

“Ku shawarci abokanan ku, ƴan'uwa da abokan hulɗar ku cewa su kiyayi yin kowace irin zanga-zanga. Ku bari kawai ku nuna musu fushin ku a lokacin zaɓe ranar Asabar."

Wani mai amfani da sunan @morningstar_305 ya rubuta, 

“Yanzun nan na kira waya gida inda aka tabbatar min da cewa masu zanga-zanga sun cinnawa bankunan Keystone da Union a Ijoku wuta.

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, hukumar ƴan sanda ba tace komai ba kan lamarin. Rahoton Naija News

A ranar Alhamis ne dai da ta gabata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanarwa da ƴan Najeriya cewa tsofaffin takardun kuɗin N500 da N1000 sun daina aiki.

Sai dai shugaban ya ƙara wa'adin amfani da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

Karancin Kuɗi Ya Sanya Harkar Lafiya Ta Taɓarɓare - NMA Ta Koka

A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar likitoci ta koka kan yadda ƙarancin kuɗi ya kawo koma baya a harkar kiwon lafiya.

Ƙungiyar tace yanzu marasa lafiya na ji a jika a dalilin ƙarancin kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng