Karancin Kuɗi Ya Sanya Harkar Lafiya Ta Taɓarɓare - NMA Ta Koka

Karancin Kuɗi Ya Sanya Harkar Lafiya Ta Taɓarɓare - NMA Ta Koka

  • Ƙungiyar likitocin Najeriya ta fito ta bayyana yadda sauya fasalin kuɗi ya sanya harkar kiwon lafiya ta samu naƙasu a ƙasar nan
  • Shugaban ƙungiyar likitocin na Jihar Kwara shine ya fito yayi wannan tsokacin
  • Sai dai shugaban yace za su tattauna da hukumomin da suka dace domin nemo hanyoyin da za a shawo kan matsalar

Ƙungiyar likitoci ta Najeriya (NMA) ta sanar da cewa sabon tsarin sauya fasalin kuɗi ya sanya harkar kiwon ƙafiya ta taɓarɓare a ƙasar nan.

Ƴan Najeriya na cigaba da fama da matsalar ƙarancin kuɗi a dalilin sabon tsarin sauya fasalin kuɗi na babban bankin Najeriya (CBN). Rahoton The Cable

Kungiyar NMA
Karancin Kuɗi Ya Sanya Harkar Lafiya Ta Taɓarɓare -NMA Ta Koka

Da yake magana a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da ƴan jarida, Ola Ahmed, shugaban NMA na jihar Kwara, yace marasa lafiya na shan wahala wajen ganin likita da samun magunguna saboda ƙarancin kuɗi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

Marasa lafiya na cikin tsaka mai wuya domin basa iya siyen magungunan da suke buƙata su cigaba da rayuwa." A cewar shugaban.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mara lafiyan dake cikin tsanancin rashin lafiya kuma baya iya samun kuɗin biyan magunguna na cikin ƙaƙanikayi."
“A yayin da hanyoyin tura kuɗi ba su cika aiki ba a wasu lokutan, wasu mutane na yin amfani da hakan ta hanyar tura 'alert' ɗin ƙarya."

Sai dai Ahmed, yace ƙungiyar zata ziyarci shugabannin asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin da hukumar kula da asibitocin jihar Kwara, domin ganin sun samu hanyar da za a magance matsalar. Rahoton Vanguard

Ya kuma ƙara da cewa ƙungiyar zata ziyarci asibitocin gwamnati da masu zaman kan su domin samar da hanyoyin da za a shawo kan matsalar.

Haka kuma, Munirat Bello, sakatariyar ƙungiyar (PSN) ta jihar Kwara, tace masu siyar da magunguna na iya bakin ƙoƙarin su wajen ceto rayuwar mutane ta hanyar bayar da magunguna bashi a dalilin ƙarancin kuɗi.

Kara karanta wannan

Ana Dab da Zaɓen 2023, Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wurin Kamfe, Sun Buɗe Wuta

"Marasa lafiyan da suka karɓi magunguna bashi za su iya biya lokacin da suka samu" Inji ta.
“Amma matsalar shine wasu mutanen basu dawowa su biya. Sai dai duk da hakan zamu cigaba da hulɗa da kwastomomin mu da marasa lafiya domin ceto rai."

Canjin Kudi Ya Jawo Karuwai Su na Kuka, Ana Samun Karancin Abokan Yin Lalata

A wani labarin na daban kuma, masu sana'ar zaman kan su sun koka kan yadda sauya takardun kuɗi ya kawo musu cikas a kasuwancin su.

Masu sana'ar sun ce yanzu samun abokan baɗalar su yayi ƙaranci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng