An Kirkiri Sauyin Naira Ne Don Durkusar Da Kasuwancin Kano, In Ji Kwamishina

An Kirkiri Sauyin Naira Ne Don Durkusar Da Kasuwancin Kano, In Ji Kwamishina

  • Gwamnatin Kano ta zargi CBN da hana bankunan kasuwanci a jihar kudi don musgunawa yan Jihar
  • Gwamnatin ta bakin kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya ce shirin gwamnan babban bankin siyasa ce tsantsa
  • Gwamnatin Jihar ta tabbatar cewa za ta yi duk mai yiwuwa don saukakawa al'ummar jihar

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano, ranar Juma'a, ta ce rashin sakar wa bankunan kasuwanci kudi daga babban bankin kasa CBN na tsawon kwana hudu a matsayin 'abin takaici', rahoton The Punch.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gidan jihar, Mallam Muhammad Garba, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tun Litinin din da ta wuce, babban bankin kasa bai bawa bankuna a jihar ko kobo ba.

Taswirar Kano
Tsawon Kwanaki 4 CBN Bai Ba Wa Bankunan Kano Ko Sisi Ba, Kwamishina. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An kirkiri sauyin naira na don durkusar da tattalin arzikin Kano, Kwamishina

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

A cewar sa, wannan mummunan shirin na gwamnan banki, Godwin Emifiele, na kirkiro dokar takaita takurdun kudi, ko ma menene kudirin, ''anyi ne don durkusar da Kano da tattalin arzikin ta, duba da irin karfin hada-hadar kasuwanci ta yau da kullum a babbar cibiyar kasuwancin ta Arewa, ta hanyar tauye bankunan kasuwanci na kudin da ya kamata a raba musu.''

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Garba ya ce babban bankin kasa CBN da ke karkashin gwamnatin tarayya, ga dukkan alamu, ya zama abin da ke shiga sha'anin siyasa ta hanyar zabar lokacin da bai dace ba don tursasa dokar da za a iya zabar lokacin da ya dace don gudanar da ita a baya.

Kwamishinan ya ce lamarin ya jefa da yawa daga cikin mutanen jihar cikin wahala ta hanyar hana su anfanar kudaden da suka yi wahalar nemowa, ''da aka kirkira da gangan don kawo rikicin da zai iya janyo dage zaben da mutane suka jima suna tsammani a sati mai zuwa.''

Kara karanta wannan

Zan Rufe Dukkan Bankunan Da Ba Su Karbar Tsaffin Kudi A Jiha Ta, Gwamna Abiodun

Sai dai, ya bayyana mutanen Kano a matsayin masu son zaman lafiya da za su iya jure wannan matsin da aka shiga.

Garba ya bada tabbacin cewa gwamnatin Jihar karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ''za ta yi duk mai yiwuwa don shawo kan lamarin.''

Dangane da batun, Legit.ng Hausa ta tuntubi wani ma'aikacin daya cikin manyan bankunan kasuwancin Najeriya da ke da rassa a Kano, inda shima ya tabbatar cewa an yi kwana hudu ba a samu kudi a bankinsu ba.

Ma'aikaci da ya nemi a sakaya sunansa ya kara da cewa iya saninsa babu wani dalili a hukumace na rashin kawo kudin sai dai ya ji kishin-kishin din cewa rashin yanayi mai kyau ne ya hana jiragen sama tashi su kawo kudin.

Kalamansa:

"Lallai mun yi kwana hudu ba mu samu kudi ba, ban da masaniya a hukumance kan jikirin kawo kudin amma na ji wai rashin kyawun yanayi ne. Mun samu yan N200 a ranar Alhamis."

Kara karanta wannan

Sokoto: Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

Bashir Ahmad ya zolaye Gwamna Ganduje kan sukar tsarin sauya naira

Mashawarcin shugaba Muhammadu Buhari kan sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad, ya zolaye gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje kan sukar tsarin sauya fasalin naira na CBN.

Ahmad, wanda ya taba neman tikitin takarar majalisar tarayya Kano ya fada wa gwamnan na Kano ya tafi CBN ya kai tsaffin kudinsa a canja masa idan na halak ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164