An Yi Dirama Yayin Da Wani Ya Taho Ofishin CBN Na Kano Dauke Na Tsaffin Kudi N50m Cikin Buhu, Bidiyon Ya Bazu
- Wani bidiyo da ya bazu ya nuna wani dan Najeriya yana hanyar zuwa ofishin CBN a Kano don kai tsabar tsaffin kudi N50 miliyan
- Mutumin wanda ba a tabbatar ko shi wanene ba ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne kuma kudinsa ne
- Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa N500 da N1000 an dena amfani da su
Wani mutum dan Najeriya ya janyo cece-kuce a daya cikin rassan babban bankin Najeriya da ke Kano lokacin da ya tafi saka tsaffin kudi na naira miliyan 50 a asusun bankin.
Bidiyon mutumin ya bazu sosai a dandalin sada zumunta inda wasu ke tambaya me yasa ya jira sai wannan lokacin zai kai kudin banki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya rika murmushi yayin da ya ke amsa tambayoyin da jami'an CBN ke masa a lokacin da ya ke hanyar shiga hedkwatar ta CBN tare da wasu maza hudu da ke dauke da buhunan kudin.
Da ya ke bada amsa, mutumin ya ce kudin nasa ne kuma shi dan kasuwa ne a jihar Kano.
Da aka masa tambaya kan dalilin da yasa sai yanzu ya ke kawo kudin, ya bada amsa da cewa:
"Ni dan kasuwa ne kuma filawa na ke sayarwa."
Bayan bidiyon ya kare a gaban ofishin na CBN, ba bu tabbas ko an bawa mutumin damar ya bada tsaffin kudin na Naira miliyan 50.
Amma, CBN ya ce babu wani mutum da zai rasa kudinsa muddin na halas ne kuma ofishinta a bude ta ke don karbar tsaffin takardun nairan.
Gwamnan jihar Kaduna ya saba umurnin Shugaba Muhammadu Buhari kan dena amfani da tsaffin kudi
A wani rahoton kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna ya yi fatali da umurnin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada na cewa a dena amfani da tsaffin naira N500 da N1,000.
El-Rufai ya bayyana hakan ne cikin wata jawabi da ya saki ga mutanen jihar Kaduna kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cikin jawabin, gwamnan na jihar Kaduna ya umurci mazauna jiharsa su cigaba da kashe tsaffin kudin har sai lokacin da kotun koli na kasa ta yanke hukunci ta ce a dena amfani.
Asali: Legit.ng