Ku Bar Tsarin Sauya Fasalin Naira Ya Yi Aikin Da Ake Fata, Emefiele Ga Yan Najeriya
- Gwamnan CBN ya gana da shugaban kasa Buhari da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilan tarayya kan tsarin sauya naira
- Mista Godwin Emefiele, ya yi kira ga 'yan Najeriya su bari wannan tsarin ya yi aiki, ya lissafo abu 3 da ake fatan zai magance
- A yau da safe, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi jawabi kai tsaye kan sabon tsarin sauya fasalin N200, N500 da N1000
Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a ranar Alhamis, ya roki 'yan Najeriya su taimaka su kyale tsarin sauya fasalin naira da gwamnati ta zo da shi ya yi aiki.
Mista Emefiele ya faɗi haka ne yayin hira 'yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kwamitin majalisar wakilai na wucin gadi kan tsarin.
Gwamnan CBN ya kara da bayanin cewa ya zauna da shugabannin bankunan kasuwanci 15 kuma ya basu umarnin su ci gaba da baiwa mutane takardun tsohon N200 nan take.
Rahoton Vanguard ya tattaro Godwin Emefiele na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Maganar gaskiya mu nan duk ma'aikata ne, muna bautawa yan Najeriya. Kowa ya ji maganar Antoni Janar kan wannan batun, shugaban kasa ya fayyace komai a jawabin kai tsaye yau da safe."
"Ina tunanin ni sai dai na yi kira ga yan Najeriya, su bari wannan tsarin ya yi aiki. Wannan tsarin guda ɗaya ne da muka zo da shi domin rage cin hanci da rashawa da kuma yawon kuɗi ba kan ƙa'ida ba."
"Wannan tsarin zai warware wasu matsaloli da suka baibaye tattalin arziki, zai rage yawan tabarbarewar tsaro a ƙasar nan."
"Waɗan nan muhimman abu 3 suna cikin kudirin wannan gwamnatin kuma suna da alaƙa da tsarin sauya Naira, saboda haka mu yi hakuri mu bari ya yi aikin da muke sa rai," inji Emefiele.
A wani labarin kuma CBN ya jero matakai uku da mutum zai bi idan yana son maida tsoffin takardun naira banki
Wannan na zuwa ne bayan babban bankin na kasa ya ssanar da cewa tun ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023 tsohon N200, N500 da N1000 suka daina amfani.
Lamarin dai ya ɗaure wa mutane kai saboda Kotun koli ta dakatar da wannan wa'adin har dai an kammala shari'ar dake gabanta.
Asali: Legit.ng