Mai Bayarwa Baya Taba Rasawa: Mai Aikin Gini Ya Kwashi Garabasa Bayan Ya Taimaki Wani Da N200

Mai Bayarwa Baya Taba Rasawa: Mai Aikin Gini Ya Kwashi Garabasa Bayan Ya Taimaki Wani Da N200

  • Wani dan Najeriya mai aikin gini ya sha jinjina a Instagram bayan ya nuna cewar shi din yana da zuciyar jin kai
  • A wani bidiyo mai tsuma zuciya, mai aikin ginin ya baiwa wani da bai sani ba kyautar kudi don ya yi kudin mota da shi
  • Da yake yaba wannan karamci da ya nuna masa, matashin ya fito da damin kudi sannan ya mikawa mai aikin ginin

Wani mai aikin gini ya samu tukwicin karamcin da ya nuna wa wani da bai sani ba a kan hanya.

Yayin da yake gudanar da aikinsa, wani mutumi ya tinkari mai aikin ginin inda ya nuna masa kamar yana cikin wani yanayi na neman taimako. A cewarsa, yana bukatar kudin hawa motar komawa gida.

Mai aikin gini
Mai Bayarwa Baya Taba Rasawa: Mai Aikin Gini Ya Kwashi Garabasa Bayan Ya Taimaki Wani Da N200 Hoto: @dexycreation
Asali: Instagram

Ba tare da kokwanto ba, mai aikin ginin ya gaggauta neman mai aikinsa ya baiwa mutumin da bai sani ba N200.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda wani ya tsiro da hanyar yin aski da cokali, jama'a sun kadu

Da yake martani ga karamcin da ya nuna masa, nan take mutumin ya sanar da mai aikin ginin cewa kawai gwada shi yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dama so yake ya ga mutum na farko da zai taimaka masa, sannan shi kuma zai mayarwa mai shi da riba a kai.

Nan take fuskar mai aikin ginin ya cika da farin ciki yayin da ya karbi kyautar kudinsa.

Jama'a sun yi martani

Captured_by_ayo ya ce:

"Tsohon kudi ne fa kada ka karba."

Ika._.marley ya yi martani:

"Ina rokon Allah ya kawo mana dauki a lokacin da bamu yi tsammani ba...Allah ya albarkace ka."

_boyspecial_ ya yi martani:

"Yawancin mutane na tunanin yan arewa mugayen mutane ne, ina fatan sun gani yanzu cewa yawancin yan arewa suna da kirki."

Zeusnation100 ya ce:

"Kana tabbatar ma duniya a kodayaushe cewa har yanzu akwai mutanen kirki a sassa daban-daban na kasarmu hatta ga karamin mutum. Nagode."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Matashi Ya Je Banki Da Ruwa a Bokiti, Ya Yi Wanka Yayin da Mutane Ke Kallonsa a Bidiyo

Tsohuwa mai shekaru 150 ta bayyana a Najeriya

A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a da dama sun cika da mamaki bayan bayyanar bidiyon wata tsohuwa yar Najeriya da ake tunanin shekarunta sun kai 150 a duniya.

An dai gano matar cikin yanayi mai kyau ga fatar jikinta na sheki wanda ke tabbatar da lallai a sha kyau da kuruciya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel