Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN
- Muhammadu Buhari ya sabawa umarnin kotun koli tun da ya haramta amfani da N500 da N1000
- A jawabin da ya yi a yau, Shugaban kasa ya ce N200 kadai za a dawo da su domin cigaba da kashewa
- Wannan akasin abin da Alkalan kotun koli su ka yanke ne a shari’ar Gwamnatin tarayya da jihohi
Abuja - Mako guda bayan kotun koli ta zartar da hukunci a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kudi, shugaban kasa ya yi wa umarnin taurin-kai.
A wani rahoto na Premium Times, an zargi Mai girma Muhammadu Buhari da daukar matakin da ya ci karo da abin da Alkalan Najeriya suka zartar.
Yayin da shugaban kasa ya amince a dawo da N200 domin a cigaba da kashewa, Buhari ya ce tsofaffin N500 da N1000 duk sun rasa matsayinsu na kudi.
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a daina mu’amala da tsofaffin N500 da N1000 da aka canza, ta yanke cewa a maida wadannan kudi zuwa bankin CBN.
Dokar CBN ta sha gaban kotun koli?
Buhari ya fake ne da sashe na 20 (3) na dokar CBN na shekarar 2007 wajen kore darajar tsofaffin N500 da N1000, duk da maganar tana gaban kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta fahimci shugaban na Najeriya da kansa ya amsa cewa ana shari’a a kotun koli.
A zaman karshe da kotu tayi a ranar Laraba, Alkalai ba su janye umarnin da suka bada ba, kenan har gobe tsofaffin Nairorin kudi ne a dokar Najeriya.
Daily Trust ta ce akalla Gwamnoni shida suke shari’a da gwamnatin tarayya a kan canjin kudi, kuma kotu ta halatta amfani da Nairorin da aka canza.
Gwamnonin da suka yi kara sun hada da Nasir El-Rufai, Yahaya Bello, Bello Matawalle, Abdullahi Ganduje, Abubakar Bello da Nyesom Wike.
An ki bin doka - Lauya
Dr. Monday Ubani wanda Lauya ne mai kare hakkin Bil Adama yana da ra’ayin dawo da N200 da shugaban kasa ya yi, bijirewa hukuncin babban kotun kasa ne.
A wata hira da aka yi da shi, an rahoto Ubani yana cewa bai ji dadin abin da ya faru ba domin ya kara nuna Muhammadu Buhari ya yi suna wajen sabawa kotu.
Ana son sayen kuri'u ne?
Shehu Sani ya ce abin da ya jawo Gwamnoni suke adawa da canjin takardun Naira da tsarin takaita yawon kudi shi ne su na son sayen kuri’u a zabe.
Tsohon Sanatan yana ganin da a ce sai bayan zabe za a sauya kudin, da babu wani ‘dan siyasa da zai kalubalanci tsarin na bankin CBN ko ya yi adawa.
Asali: Legit.ng