Muhimman Batutuwa 10 da Aka Fahimta Daga Jawabin Shugaban Kasa Kan Canjin Naira

Muhimman Batutuwa 10 da Aka Fahimta Daga Jawabin Shugaban Kasa Kan Canjin Naira

Abuja - A ranar Alhamis aka wayi gari da sauraron Mai girma Muhammadu Buhari yana yi wa ‘Yan kasa jawabi a game da batun sauya kudin.

Mun tsakuro kanun bayanin da shugaban Najeriyan ya yi a jawabin da ya gabatar a dazu.

1. N200 ta dawo

Babbar sanarwar da aka ji a jawabin na yau shi ne za a fito da tsofaffin N200 a rika kashewa daga yanzu zuwa ranar 10 ga watan Afrilu 2023.

2. Babu maganar N500, N1000

Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa N500 da N1000 sun daina aiki a matsayin takardun kudi a Najeriya duk da cewa za a sake dawo da N200.

3. Sababbin kudi sun zo kenan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya kare bankin CBN da ya fito da sababbin kudi, ya ce hakan ya zama dole domin kudin da ke wajen asusun bankuna sun yi yawa.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

4. Buhari ya bada hakuri

Jaridar ta ce Muhammadu Buhari ya ba al’umma hakurin wahalhalun da suka shiga, ya bada umarnin CBN ya yawaita samuwar kananan kudi.

5. Dalilin canza kudi

Buhari ya dauki lokaci wajen bayanin yadda canjin zai bunkasa tattali, magance tsadar kaya, rashin tsaro, da rage adadin marasa zuwa banki.

Shugaban Kasa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ofis Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

6. Amfanin sababbin Nairori

Gwamnati ta ce sababbin Nairorin za su habaka darajar Naira, su rage kudin da ke yawo tare da kawo saukin farashi da samun bashi da hana sace-sace.

7. Doka za tayi aiki

Shugaba Buhari ya bada umarni CBN su hada-kai da hukumomin yaki da rashin gaskiya wajen cafke fuk wadanda suke kawowa wannan tsari tasgaro.

8. Kira ga al’umma

Jawabin shugaban kasar ya kunshi kira ga ‘Yan Najeriya suyi hakuri domin fahimtar manufofin tsarin, ya ce za a fita daga mawuyacin halin da ake ciki.

9. Magajin Buhari zai amfana

A watan nan za a gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya, an ji canza Nairorin da aka yi ya rage tasirin amfani da kudi wajen lashe zabe.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Da alamu an kusa daina ganin tsabar kudi, CBN zai iya kakaba wata hanyar biya

10. A guji rikicin zabe

A karshe, jawabin shugaban kasar ya kunshi kira ga mutane su zabi wanda suke so ba tare da jin tsoro ba, ya ce a guji jawo tashin-tashina a zabe mai zuwa.

Kuskuren da aka yi - Sanata

An ji labari Shehu Sani ya ce a lokacin da majalisar tarayya ta amince da kudirin ya zama doka, ba a tafka muhawara sosai domin a fahimci tasirin tsarin ba.

Sanata Shehu Sani ya nuna ba a wayar da kan mutane sosai ba, sai kwatsam yanzu aka fahimci cewa sauyin kudin da aka yi yana tasiri a kan rayuwar kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng