Ku Guji Zanga-Zangar Tashin Hankali: Tinubu Ya Yi Kira Ga Matasa Yayin da Karanci Naira Ke Kara Ta’azzara
- Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, bai ji dadi ba yayin da zanga-zanga ta barke a manyan jihohin Najeriya saboda karancin kudi da man fetur
- Tinubu ya roki yan Najeriya da su kara hakuri da CBN kasancewar ana kokarin ganin sabbin takardun kudin sun wadata a kasar
- Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bukaci jama'a musamman matasa da su guji duk wani rikici sannan su mayar da hankali kan babban aiki da ke gaba, zaben shugaban kasa na 2023
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, ya magantu kan halin da ake ciki a kasar.
Tinubu ya bukaci yan Najeriya da su guji duk wani nau'i na rikici yayin da karancin naira ke kara ta'azzara.
A wata sanarwa da daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Bayo Onanuga ya saki a Facebook, Tinubu ya bayyana halin da ake ciki a matsayin wanda zai zama tarihi nan ba da dadewa ba.
Tinubu ya yi kira ga kwantar da hankali yayin da jihohin Najeriya ke zanga-zanga kan karancin kudi
Dan takarar shugaban kasar ya tausayawa yan Najeriya kan radadin da suke fuskanta wajen cire kudi daga bankuna da na'urar ATM.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya yi jawabin ne a wata sanarwa dauke da sa hannunsa.
Tinubu ya ce:
"Ina bakin ciki da rahotan zanga-zangar tashin hankali da aka samu a yankunan kasarmu a yau musamman a jihohin Delta, Oyo, Kwara da Edo. A Delta, an samu rahoton kone-kone da fashe-fashen bankuna.
"Na tausayawa daukacin yan Najeriya da ke cikin kunci na rashin samu kudadensu daga bankuna da ATM don gudanar da harkokinsu na yau da kullun. Na kuma tausayawa bankunan da lamarin sauya kudi na CBN ya ritsa da su.
"Ku kwana da sanin cewa wannan lokaci zai wuce nan ba da jimawa ba kasancewar gwamnatinmu na tarayya da jiha suka aiki don shawo kan kalubalen da ake ciki a yanzu."
Jama'a sun yi martani
Orlarwaley Jamine Cole ya ce:
"Asiwaju shine mutumin da ya fahimci dabarun da Najeriya ke bukata ta bangaren shugabanci da manufa. Dan Allah mu shirya, bayar da goyon bayanmu ga wanda ya shirya jan ragamar kasarmu mai albarka mai suna Najeriya! Ta yadda al'ummar kasar za su samu ingantacciyar rayuwa."
Akinduro Akinrolabu ya ce:
"Allah ya albarkaci Tinubu kan wannan kalaman karfafa gwiwa na kishin kasa."
Dennis Samson:
"Nagode yallabai Sanata Bola Hamed Tinubu."
An yi zanga-zanga a jihohin Ondo, Delta da Kwara kan karancin naira
A gefe guda, mun kawo a baya cewa wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin kasar da suka hada da Ondo, Delta da Kwara kan karancin tsoffin kudi da kuma kin karbar tsoffi da yan kasuwa ke yi.
Asali: Legit.ng