Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai
- Nasir El-Rufai ya ce jami’an gwamnatin tarayya na neman su domin ayi sulhu kan karar da suka kai
- Gwamnoni su na shari’a da gwamnatin kasar a kotun koli a dalilin sauya manyan takardun kudi
- El-Rufai ya nuna ba su karbi tayin da aka gabatar masu ba, za su nemi kotun koli ta yanke hukunci
Abuja - A ranar Laraba, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa jami’an gwamnatin tarayya su na rokon su yi sulhu da gwamnonin da suka shigar da kara a kotu.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fitar da jawabin musanya rade-radin cewa gwamnoni sun yi zama da gwamnatin tarayya a kan batun canjin kudi.
A rahoton da aka samu, Muyiwa Adekeye wanda ya fitar da jawabi a madadin Gwamnan Kaduna ya ce takwarorinsa ba su yi zama da shugaban kasa ba.
Jawabin ya ce gwamnatin tarayya tana so ne a ba ada damar cigaba da amfani da N200 kadai a matsayin takardar kudi daga yanzu har zuwa 10 ga Afrilu.
CBN sun lalata tsofaffin kudi?
A cewar Gwamnan, gwamnatin tarayya na ikirarin CBN ya lalata tsofaffin N500 da N1000 da aka karba, amma wadanda suke da na su, za sui ya kai masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidan talabijin na Channels ta rahoto Malam El-Rufai ya na cewa amfani da N200 kadai ba zai isa ba idan aka yi la’akari da irin wahalar da jama’a suke sha.
Tun farko Gwamnan bai yarda cewa bankin CBN ya kona ragowar kudin ba, kuma ya ce za a bukaci akalla shekara daya kafin a iya buga Naira tiriliyan 1.
Alkaluman da ake fitarwa ba daidai ba ne, El-Rufai ya kara da cewa masu neman a sasanta da yawun gwamnati su na fitar da bayanan da ba gaskiya ba.
Babu maganar yin sulhu - El-Rufai
Yayin da gwamnatin tarayya ta bukaci a sasanta ba tare da an je kotu ba, Gwamna El-Rufai ya nuna kai-tsaye suka yi watsi da bukatun da aka gabatar.
A rahoton Daily Trust, an fahimci Gwamnan ya zargi gwamnatin kasar da rashin gaskiya, ya ce su na sa ran kotun koli tayi masu adalci a wannan shari’a.
A karshe, El-Rufai ya ce zai yi wa mutanen jihar Kaduna cikakken bayanin halin da aka shiga da kuma tasirin tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin kudi.
Kaduna vs Gwamnatin kasa
A wani labari na dabam, kun ji cewa wani babban Lauya, Abdulhakeem Mustapha ya tsayawa Gwamnatin Kaduna, ya kai karar gwamnatin tarayya a kotu.
Gwamnatin Buhari ta dauko hayar Ministan shari’a a Gwamnatin Obasanjo domin ya kare ta. Kanu Agabi (SAN) ya musanya zargin Barista Mustapha (SAN).
Asali: Legit.ng