Karancin Naira Ya Sa Hukumar Jarrabawa Ta JAMB Ta Tsawaita Wa’adin Rajistar Jarrabawa
- Hukumar jarrabawa ta JAMB ta ce ta tsawaita wa'adin cike fom din UTME saboda karancin Naira
- Hukumar ta ce ta tsara yadda za ta ke yiwa mutane 100,000 rajista a rana daya saboda saukaka yin rajista
- Najeriya na ci gaba da shiga wani yanayi tun bayan da aka fara batun sauyin kudi, musamman a kasuwanni
Hukumar shirya jarrabawar shiga jami'a ta JAMB ta tsawaita rajistan UTME na 2023 da mako daya, farawa daga ranar 15 ga watan Faburairu, Daily Trust ta ruwaito.
Tsawaita wa'adin na zuwa ne, a cewar hukumar saboda da yawan daliban da ke da sha'awar rubuta jarrawar basu samu damar siyan ePIN ba saboda karancin Naira.
A halin da ake ciki, za a rufe siyar da ePIN a ranar Litinin, yayin da za a daina rajistan UTME din a ranar Laraba 22 ga watan Faburairu.
A tun farko, JAMB ta tsara za a siyar da ePIN na UTME 2023 zuwa ranar 14 ga watan Faburairu, za a rufe rajista kuma a ranar 17 ga watan Faburairu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda rajistar UTME na bana a kasance
Kakakin hukumar Jamb, Dr. Fabian Benjamin ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ya zuwa ranar Takata, akalla mutane 1,527,068 ne suka yi nasarar siyan ePIN.
Hakazalika, daga cikin wancan adadin akwai 168,748 da suka nuna sha'awar yin jarabawar gwaji ta Mock gabanin jarrabawar gaske ta UTME, Premium Times ta ruwaito.
A cewarsa, yanzu haka hukumar ta tsara yadda za ta yiwa mutane 100,000 rajista a rana daya, kamar yadda rahoto ya bayyana.
A bangare guda, ya ce hukumar za ta yi karin wa'adin ne saboda ba wadanda basu yi rajista ba damar yi saboda ana fuskantar matsalar kudi a kasar.
Akwai kudi a CBN, bankuna sun ki dauka
A wani labarin, kun ji yadda CBN ya musanta batun cewa akwai karancin sabbin Naira a hannun jama'a.
Bankin ya shaida cewa, kudi na nan a kasa, bankuna sun ki zuwa su dauka ne saboda wasu dalilansu.
Gwamnan CBN ya ce, akwai adadin da ake tsammanin kowane banki ya zo ya dauka, amma ba a zuwa.
Asali: Legit.ng