Rana Mai Tarihi: Sanusi Ya Shiga Kano a Karon Farko Tun Tsige Shi Daga Sarauta
- A yau aka ga abin da ba a saba ba a garin Kano, tubabben Sarki Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara
- Malam Muhammadu Sanusi II yana kan hanyarsa ta zuwa Jigawa ne, dole ta sa ya tsaya a Kano tukuna
- Masoya sun tarbo Khalifa tun a filin jirgi, ya ci karo da dinbin masoyansa har zuwa gidan tsohuwarsa
Kano - Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara ta musamman zuwa ga mahaifarsa a yau Laraba, 15 ga watan Fubrairu 2023.
Legit.ng Hausa ta fahimci Muhammadu Sanusi II ya je garin Kano ne ta jirgin sama, inda masoyansa da wasu dogarai suka yi masa maraba.
Bidiyoyi da ke yawa a dandalin sada zumunta sun nuna masu kaunar tsohon Sarkin su na rokon Ubangiji ya ba shi damar da zai dawo sarauta.
A kan tituna kuwa, an ga jama’a su na matukar farin ciki da shigowar Muhammadu Sanusi II. Yayin da ya zauna a gida, an yi ta masa wakoki.
Sanusi II zai je ta'aziyya Dutse
Jaridar Daily Trust ta ce Mai martaban ya na isowa garin Kano ya wuce gidan mahaiyarsa da ke titin Ibrahim Dabo a birni ya gaida ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana tunanin Sarkin da aka tunbuke zai wuce garin Dutse a jihar Jigawa ne domin ya yi wa masarautar kasar rashin Nuhu Muhammad Sanusi.
Sanusi II zai yi wa fadar ta’aziyyar mutuwar Mai martaba Nuhu Muhammad Sanusi wanda ya rasu bayan shekara da shekaru yana gadon sarauta.
Shekaru 3 ba ya Kano
Tun da Abdullahi Ganduje ya sauke shi daga gadon sarauta, Punch ta ce wannan ne karon farko da Sarkin na 14 zai taka kafarsa a birnin Kano.
“Ba zan iya zuwa Jigawa kai-tsaye a jirgin sama ba a sakamakon yanayin hazo da ake yi a yau.
Daruruwan mutane suka duro wajen, suka bukaci akalla in kai wa mahaifiyata ziyara domin in gaida ta, kuma na yi hakan.”
- Muhammadu Sanusi II
Khalifan na Tijjaniyyah ya shaida cewa bisa hukuncin kotu da dokar kasa, yana da damar da zai ziyarci duk wata jihar da ya ga dama a Najeriya.
Canjin kudi a Najeriya
A rahoton da aka fitar dazu, an ji Godwin Emefiele ya ambaci nasarar canza kudi da aka samu da kuma sharrin ‘yan siyasa ke kitsawa saboda zabe.
Gwamnan babban bankin kasar ya ce ‘yan siyasa sun dage wajen ganin sun batawa tsarinsa suna, don haka suke sayen kudin da za su ayi a 2023.
Asali: Legit.ng