Fusatattun Mutane Sun Babbaake Bankuna a Jihar Delta Saboda Karancin Naira
- Zanga-zanga ta barke a jihar Delta sakamakon kuncin da yan Najeriya suka shiga kan karancin takardun naira a hannu
- Bayanai sun nuna cewa mutane sun fara banka wuta a bankuna da ATM a yankin karamar hukumar Udu
- Gwamna Okowa ya roki mazauna su ƙara hakuri domin masu alhaki na kokarin ƙara yawan kuɗin a hannu
Delta - An shiga yanayin tashin hankali a jihar Delta yayin da mutane suka tunzura suka fantsama kan tituna da manyan hanyoyi domin nuna takaicinsu kan halin ƙuncin da suka shiga.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa fusatattun mutanen sun banka wa wani Banki wuta a babban Titin Udu, karamar hukumar Udu a jihar Delta.
Bugu da ƙari, sun kakkarya wasu allunan kamfen yan takara a yankin. A cewar wani mazauni karancin sabbin naira da kuma dena karban tsoffin ya harzuƙa mutane.
Mutumin mai suna, Mista Martins Alala, ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Mu yan kasa ne da ke nuna adawar mu da karancin sabbin kuɗi da kuma haramta amfani tsofaffin takardun naira. An kewaye mu da wahala da ƙunci."
"Yanzu da nake magana mun bankawa ATM wuta a Access Bank da First Bank, yanzu muna harin Eco Bank a DSC, ya zama tilas bankuna su ji raɗaɗin da muke ji."
"Muna da kuɗi amma ko ganin takardun naira tsoho da sabo bama yi balle mu yi amfani da su, dukkansu basu kwata-kwata."
Bayanai sun nuna cewa dakarun yan sanda sin mamaye yankin DSC da nufin hana fusatattun masu zanga-zangan zuwa su lalata kadarorin gwamnati.
Kowa ya kwantar da hankalinsa - Gwamna Okowa
Gwamna Ifeanyi Okwa na jihar Delta kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a PDP ya yi kira ga mazauna jihar da Najeriya baki ɗaya su kwantar da hankulansu.
Wannan na zuwa ne yayin da zanga-zanga ta ƙara tsananta a yankin karamar hukumar Udu, inda abun ya kai ga taɓa bankunan kasuwanci.
Kalaman kwantar da hankali daga Okowa na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na Delta, Mr Charles Aniagwu, ya fitar a Asaba.
A ruwayar Punch, Sanarwan ta ce:
"Muna kira ga 'yan uwa maza da mata a sassan jihar nan su kwantar da hankulansu duk da wahalhalun da suke fama da sakamakon karancin naira a hannu."
"Gwamnatin ta san halin da kuke ciki amma muna rokon ku kwantar da hankula domin masu alhakin sauya kuɗin sun ɗauki matakan ƙara yawan kuɗin domin yaye muku wahala."
Bamu ɗauki matsaya ba har yanzu - FG
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya da CBN Zasu Yi Nazari Kan Halascin Tsoffin Naira Gobe
Gwamnatin Buhari ta ce tana jiran hukuncin Kotun koli kafin ta ɗauki mataki kan wa'adin amfani da tsohon N200, N500, da N1000. Mallam Garba Shehu ya ce FG da CBN zasu ƙara nazari kan halin kuncin da ake ciki bayan an karkarshe shari'a a Kotu.
Shin Mutane Sun Yi Asara Kenan? Matakai 3 da Zaku Bi Ku Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika
Asali: Legit.ng