Wani Jigo a Jam'iyyar APC Ya Caccaki Shugaba Buhari Kan Ƙarancin Kuɗi

Wani Jigo a Jam'iyyar APC Ya Caccaki Shugaba Buhari Kan Ƙarancin Kuɗi

  • Wani babban jigo a jam'iyyar APC ya koka kan yadda sauya fasalin kuɗin naira ke kawo naƙasu ga mutanen yankunan karkara
  • Jigon na jam'iyyar APC yayi nuni da cewa lokaci yayi da ƴan Najeriya za su ɗagawa shugaba Buhari yatsa kan wanann sabon shirin
  • Tun lokacin da aka fara ƙarancin kuɗi a ƙasar nan, mambobin APC sun fi kowa nuna ɓacin ran su kan lamarin

Mataimakin darekta na ɓangaren harkokin noma a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Retson Tedheke, ya bayyana cewa sabon tsarin sauya fasalin naira na CBN, na durƙusar da sana'o'i a yankunan karkara.

Ya bayyana cewa lokaci yayi da ƴan Najeriya za su ƙalubalanci shugaba Buhari, tunda ya ƙi ya saurari koke-koken da mutane da dama suka yi masa. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Buhari Ya Canza Shawara, FG Da CBN Zasu Duba Yuwuwar Tsawaita Wa'adin Naira

Buhari
Wani Jigo a Jam'iyyar APC Ya Caccaki Shugaba Buhari Kan Ƙarancin Kuɗi
Asali: Facebook

Mr Tedheke, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya sanya a Twitter, inda yace shugaba Buhari yana azabtar da mutanen karkara da wannan sabon tsarin. Ya bayyana cewa mutane da dama sun kasa biyan haƙƙoƙin ma'aikatan su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mutane da dama na mutuwa saboda yunwa a ƙauyakun mu, babban abinda yafi ciwo shine shugaba Buhari yana kiran kan sa shugaban ƙasa. Shugaba Buhari yana kiran kansa da shugaban ƙasa na talakawa.
Ta ya hakan zata kasance bayan yana halaka manoma a karkara. Ni manomi ne wanda yake da sama da manoma 500 a ƙarƙarshin sa. Mun kasa biyan su haƙƙoƙin su. Da yawa daga cikin su, ba su da asusun ajiya na banki.
"Ko dai shugaban ƙasa ya kurumce.. Lokaci yayi da ƴan Najeriya zasu ɗaga masa yatsa su ce masa wannan mulkin dimokuraɗiyya ne, mu muka zaɓe ka."

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Obi Ko Kwankwaso? Gwamnatin Amurka Ta Magantu Kan Goyon Bayan Wani Ɗan Takara a Zaben 2023

Mambobin jam'iyyar APC sun fi kowa nuna ɓacin ran su kan ƙarancin kuɗin da ake fama da shi wanda shirin sauya fasalin kuɗin naira na CBN ya haifar.

A cewar su, wahalar da ƙarancin kuɗin ta haifar, ka iya sanya ƴan Najeriya su juya wa jam'iyyar su baya a lokacin zaɓe.

Gwamnan Bankin CBN Ya Bayyana Inda Sababbin Kudin da Aka Buga Suka Shige

A wani labarin na daban kuma, gwamnan CBN ya bayyana inda sabbin kuɗin da aka buga suke maƙalewa.

Godwin Emefiele ya ce sun lura wasu ‘yan siyasa su na sayen sababbin N200, N500 da N1000 domin manufar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida