Karancin Naira: Fusataccen Matashi Ya Kai Ruwa Bokiti Daya Banki, Ya Yi Wanka a Bidiyo
- Wani bidiyo mai tsawon sakan 44 ya hasko wani dan Najeriya yana wanka a bainar jama'a a gaban wani banki
- Baya ga zuwa da bokitin ruwa, soso da sabulu, mutumin ya kuma zo da tabarma, matashin kai da yar karamar jaka
- An yi hasashen cewa mutumin ya isa wajen ne don karbar kudinsa yayin da ake fama da karancin naira a kasar
Yayin da ake ci gaba da fama da karancin naira a kasar, an gano wani mutumin yana wanka a gaban wani banki.
Shafin @freemanghettosoja ne ya wallafa bidiyon mai tsawon sakan 44 a TikTok kuma an yi hasashen cewa mutumin ya je wajen ne don karbar wasu tsabar kudi.
Mutanen da ke wajen sun cika da mamaki cewa mutumin ya isa bankin da bokitin ruwa, kwaryar soso da sabulu.
Mutane na kallon matashi yana wanka a gaban banki yayin da ake fama da rashin kudi
Bai tsaya a nan ba, matashin ya kuma tanadi tabarmarsa, matashin kai da wasu yan kayayyakinsa na amfani da karamar jaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama a bankin suna ta kallo cike da mamaki yayin da mutumin ya wanke duk wani sassa na jikinsa da soso sai kace yana cikin bandakin gidansa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yan Najeriya da dama ke fama da rashin tsabar kudi don gudanar da harkokinsu na yau da kullun yayin da manufar CBN ke ci gaba da aiki.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Ifeyinwa Eucharia Uyanneh ta ce:
"A nan za ka dunga bacci da wanka har sai kudinka ya fito."
@àbèèbiade ya yi martani:
"Amma da gaske sauyin da Buhari ya yi mana alkawari shi muke gani. Chanji ba na wasa ba."
@nne199 ta ce:
"Wannan bankin first bank na Enugu ne da ke liberty."
@prohetress Amara okeke ta ce:
"Ba zan taba mantawa da wannan lamari na kudi ba."
@i33ify ta ce:
"Wannan mutumin na son janye hankalin mutane daga wajen karbar kudinsu."
Yan Najeriya sun yi layi a gaban ATM da karfe 2 na tsakar dare
A wani labarin, mun kawo cewa wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno yadda wasu daruruwan yan Najeriya suka jeru a kan layin ATM da karfe 2 na tsakar dare.
Asali: Legit.ng