Dalilin Canza Kudi, Mai Martaba Ya Koka da CBN, Babu N20, 000 a Cikin Fadar Sarki
- Sarkin kasar Iwo ya ce ba zai iya bugun kirji ya ce za a samu ko da N20, 000 a cikin fadarsa ba
- Basaraken ya ce tsarin sauya manyan takardun kudi ya jawo mutanen Najeriya sun shiga kunci
- Abdurosheed Akanbi yana so shugaban kasa ya umarci Godwin Emefiele a buga sababbin kudi
Osun - Mai martaba Sarkin Iwo, Oba Abdurosheed Akanbi ya bayyana cewa halin da aka shiga na karancin kudi ya shafi harkar gudanar da fadarsa.
A ranar Talata, Vanguard ta rahoto Abdurosheed Akanbi yana bayani a kan canjin kudi, a nan ya bayyana cewa yanzu haka babu N20, 000 a fadarsa.
Basaraken yake cewa tsarin sauya manyan takardun kudi na gwamnatin tarayya ya yi sanadiyyar da mutanen Najeriya suka shiga cikin matsin lamba.
Ganin yadda al’umma suke wahala a yau, Sarki Abdurosheed Akanbi ya roki gwamnatin Muhammadu Buhari ta rage radadin da talaka ya shiga.
Ranar masoya ta Duniya
Rahoton ya ce Mai martaban ya yi kiran ne a wajen yin bikin ranar masoya a jihar Osun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sarkin ya bukaci Muhammadu Buhari ya yi amfani da damar ranar masoya ta yau, ya yi kira ga Gwamnan CBN ya samar da isassun sababbin Nairori.
Akanbi yake cewa shi Sarkin talakawa da masu wadata ne, saboda haka yake so tursasa Godwin Emefiele ta yadda babban bankin CBN zai buga kudi.
A ranar da masoya ke biki, Sarkin ya gana da marasa galihu inda ya ce ba a tunawa da su. Punch ta ce ya yi kaca-kaca da wannan tsari da ya kira bagidaje.
Tare da Uwagidarsa, mai martaban ya dauki wata al’ada ta kai wa wadannan Bayin Allah marasa karfi ziyara a duk rana irin ta yau da masoya ke murna.
Kira ga Gwamnati - Sarkin Iwo
“Ina fatan Gwamnatin tarayya za tayi amfani da wannan rana domin kara kaunar al’umma. ‘Yan Najeriya su na shan wahala.
A matsayin Sarki, ba zan iya bugun kirji cewa ina da madarar kudi na N20, 000 ba. Idan ana bi na bashi a banki, ruwa zai shiga.
Amma yanzu su na rike kudi na, ba tare da an biya ni ruwa daga kudin ba. Wannan adalci ne?”
Sabon Sarkin Kontagora
Kun samu labari cewa kasar Kontagora ta samu Sarki na bakwai a sakamakon rasuwar Mai martaba Sa’idu Namaska a Satumban shekarar 2021.
Sarki Muhammadu Bararu Mu’azu II wanda ya karbi sandar girma, jikan Umaru Nagwamatse ne, kakansa Sarki Muazu Ibrahim ya yi sarauta a baya.
Asali: Legit.ng