Sabon Sarki ya Gaji Karagar Kakansa Bayan Jiran Kusan Shekaru 50 a Kontagora
- An haifi Muhammadu Barau Mu’azu II ne shekaru kusan 50 da suka wuce a kasar Kontagora
- Sabon Sarkin ya fara karatun boko a karamar hukumar Magama, kafin ya je garin Kontagora
- Muhammadu Bararu Mu’azu II jika ne a wajen Mu’azu Ibrahim wanda ya yi Sarki kafin Namaska
Haihuwa da karatun boko
Niger - An haifi Mai martaba Muhammadu Barau Mu’azu II a shekarar 1974. Mahaifinsa bai yi sa’ar zama Sarki ba duk da cewa ‘dan gidan Sarki ne.
Kakansa shi ne Sarkin Sudan, Mu’azu Ibrahim wanda jika ne a wajen Ibrahim Nagwamatse.
Muhammadu Barau Mu’azu II ya yi karatun firamare daga 1980 zuwa 1986 a makarantar firamaren da ke garin Ibeto, daga nan ya tafi sakandare.
Mai martaba ya samu shaidar karatun sakandare a makarantar sakandaren gwamnati ta Kontagora da ya halarta tsakanin shekarar 1986 da 1992.
Tsakanin 1994 zuwa 1997, Muhammadu Barau Mu’azu II ya na makarantar koyon karantarwa watau FCE da ke garin Kontagora, a nan ya samu NCE.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shekaru bayan nan, Mai martaba yana da Digiri harkar gudanar da kasuwanci daga wata babbar makarantar a Jamhuriyyar Benin da aka kafa ta a 2009.
Aiki da kasuwanci
Sabon Sarkin ya rike babban Manaja a kamfanin Salwa Global Company, har ya zama shugaba.
Wajen aiki da kasuwanci, Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu ya yi hulda da manyan Attajirai irinsu Alhaji Aliko Dangote da Kanal Sani Bello mai ritaya.
Wadannan aikace-aikace sun kai Sarkin Sudan kasashen Nijar, Ghana, Kenya, da Masar, ya je Turkiyya, Landan, Sin, Saudi Arabiya, Jamus da Amurka.
Zama Sarki a 2021
Bayan rasuwar Sa’idu Namaska a shekarar 2021, sai Gwamnatin Abubakar Sani Bello ta amince da Muhammadu Barau Muazu III a matsayin magajinsa.
Kakansa, Mu’azu Ibrahim shi ne Sarki na 5 wanda ya yi shekaru kusan 13 daga 1961 zuwa 1974 a gadon sarauta. A shekarar da aka haifi sabon Sarki, ya rasu.
Wazirin Kontagora, Madawakin Kontagora, Galadiman Kontagora, Magayakin Kontagora, Kofa ne ‘yan majalisar Sarkin da suka amince da nadinsa.
Kwankwaso ya Kontagora
An ji labari bayan ya ziyarci garuruwan Minna, Bida, da New Bussa, Rabiu Musa Kwankwaso ya je Kontagora, ya gaida sabon Sarki Muhammad Barau.
‘Dan takaran Shugaban kasar na Jam’iyyar NNPP, ya yi amfani da damar wajen yin kamfe a garin, ya soki tsarin canza kudi da babban bankin CBN ya kawo.
Asali: Legit.ng