Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Yayin da ake cikin ruɗani kan natakin bankunan kasuwanci na kin karban tsoffin takardun naira, akwai wasu hanyoyi uku da za'a bi don maida kuɗin banki.

Bankunan sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya basu wa'adin 10 ga watan Fabrairu, 2023 su rufe karban kuɗin.

A ranar Talata gwamnan babban bankin ya jaddada cewa babu bukatar tsawaita wa'adin tsohon naira a Najeriya.

Tsohon kudi.
Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Emefiele ya faɗi haka ne duk da umarnin Kotun koli na ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun naira har zuwa 15 ga watan Fabrairu, lokacin da zata saurari ƙarar da gwamnoni suka shigar.

Legit.ng Hausa ta haɗa maku matakai uku da zaku bi wajen maida tsohon kuɗin ku a rassan CBN da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Cike Fam ɗin CBN

Da farko zaku shiga safin yanar gizo-gizo na CBN ku cike Fam daga nan za'a ba ku wasu lambobi ko kuma mutum zai iya zuwa reshen CBN na jiharsa ya karɓi Fam ɗin ya cike.

2. Katin shaida (I.D Card)

Idan zaku je, ku tafi da katin shaidar zama ɗan kasa ko wasu katunan shaida kamar Katin zaɓe.

3. Za'a baku takardan Tela

Na karshe, bayan kun gama cike Fam din, CBN zai baku takardar shaidar cike fam (Teller) kuma zai karbi tsoffin takardun naira da kuke son aje wa domin sa muku a Asusun banki.

Kwanturolan CBN na jihar Bauchi, Haladu Idris Andaza, shi ne ya bayyana waɗan nan matakan da 'yan Najeriya zasu bi ranar Talata yayin da ya tabbatar da cewa tsohon naira ya daina amfani tun 10 ga wata.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Da alamu an kusa daina ganin tsabar kudi, CBN zai iya kakaba wata hanyar biya

A wani labarin kuma Babban bankin ƙasa CBN ya bayyana tsoffin N200, N500 da N500 sun daina amfani tun ranar Jumu'a da ta wuce

Yan Najeriya sun tsinci kansu cikin ruɗani da rashin tabbas kan sahihin wa'adin daina amfani da kuɗin bayan Kotun Koli ta yanke hukunci.

Sai dai a yau Talata, CBN ya tabbatar da cewa kuɗin sun rasa martabarsu na zama halastattun naira, sai dai akwai hanyar da mutane zasu bi gudun yin asara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262