Gwamna Matawalle Ya Gargadi Bankuna Su Guji Boye Takardun Sabbin Naira
- Gwamna Matawalle ya kai ziyarar ba zata Hedkwatar CBN ta Gusau da wasu bankunan kasuwanci biyar
- Yayin wannan rangadi, gwamna ya gargaɗi manajoji su guje wa boye sabbin takardun naira ko su fukanci fushinsa
- Matawalle ya kuma roki CBN ya wadata bankuna da sabon naira domin yaye wa jama'a kuncin da suka shiga
Zamfara - Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya gargaɗi bankunan ajiyar kuɗi a jihar su guji boye sabbin takardun naira guda uku da aka sauyawa fasali.
Gwamna Matawalle ya yi wannan gargaɗin ne ranar Litinin yayin da ya kai ziyarar ba zata zuwa reshen babban bankin Najeriya (CBN) da ke Gusau, babban birnin Zamfara.
Baya ga CBN, gwamnan ya kai makamanciyar wannan ziyarar bankunan ajiyar kuɗi akalla 5 domin gane wa idonsa wahalhalun da Zanfarawa ke sha wajen neman sabbin kuɗi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na ofishin gwamna, Jamilu Birnin Magaji, ya fitar ranar Talata a Gusau, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan, Birnin Magaji ya ce Gwamna ya kaɗu da ganin dogon layin mutane a jikin ATM yayin da ake tsaka da ƙarancin sabbin naira da rashin tabbas a jihar.
Wane bankuna Matawalle ya kai ziyarar ba zata?
Bugu da ƙari, Sakataren watsa labaran ya bayyana Bankunan da Matawalle ya ziyarta wanda suka ƙunshi, Hedkwatar CBN dake Gusau, United Bank for Africa (UBA), Jaiz, Eco da kuma First Bank.
Jamilu Birnin Magaji ya ce:
"Lokacin ziyarar Matawalle ya gargaɗi shugabannin Bankuna su guji mummunar ɗabi'ar ɓoye sabon naira. Ya kuma umarci bankunan su zuba sabbin naira a ATM da kuna Kanta."
Duk bankin da muka kama da laifi zamu kwace filnsa - Matawalle
A cikin sanarwan, an hakalto Matawalle na gargaɗin Manajojin banki cewa gwamnatinsa ba zata tsaya wata-wata ba zata soke lasisin mallakar filin duk bankin da ba zai taimaki al'umma ba.
Tun da fari a CBN, Gwamnan ya roki Kwanturolan babban banki ya tabbata sun wadata bankuna da sabbin kuɗi ta yadda zasu gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda Guardian ta rahoto.
CBN: Tsofaffin Takardun N200, N500 da N1000 Sun Daina Amfani a Najeriya
A wani labarin kuma CBN ya bayyana cewa tuni tsoffin takardun naira suka daina amfani a Najeriya
Kwanturolan CBN na jihar Bauchi, ya ce har yanzun mutane na da damar ɗaya yal ta ajiye tsohon naira a asusun bankunansu idan suka bi ƙa'idoji.
A yan kwanakin nan da yawan 'yan Najeeiya sun shiga ɗar-ɗar da rashin tabbas game da wa'adin haramta kuɗin.
Asali: Legit.ng