Ba a Gama da Rikicin Kano Ba, Katafaren Kanti a Abuja Ya Ki Karbar Tsoffin Naira
- Labarin da muke samu ya bayyana cewa, an samu wani kantin da ke kin karbar tsoffin kudin Naira a Abuja
- Kotun koli a Najeriya ta ba da umarnin a ci gaba da karbar tsoffin kudade tare da sabbin a hade zuwa 15 ga wata
- Jihar Kano ta garkame wani kantin siyayya da ke kin karbar tsoffin kudade duk kuwa da umarnin kotun
Wuse, Abuja - Yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin sabbin Naira, wani katafaren kantin siyayya a Wuse 2 da ke Abuja ya daina karba da tu’ammuli da tsoffin takardun Naira.
An ruwaito cewa, kantin na H-Medix ya daina karbar tsoffin Naira na N200, N500 da N1000 duk kuwa da umarnin ci gaba da amfani dasu.
A cewar rahoton Aminiya, an ga takardar ke bayyana daina karbar tsoffin kudaden a like a jikin kofar shiga kantin.
A cewar sanarwar, kamtin H-Medix zai daina karbar N200, N500 da N1000 tsofaffi daga ranar 10 ga watan Faburairu; umarnin CBN na baya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya batun umarnin kotu na ci gaba da amfani da tsoffin kudade?
Da wakilin Aminiya ya so jin dalilin yin haka duk da cewa kotu ta ce a ci gaba da karbar kudaden har zuwa 15 ga watan Faburairu, ma’aikaciyar kantin ta ce hukumar gudanar da kantin ne ya ba da umarnin yin hakan.
Hakazlaika, ta ce hukumar ta kafa hujja da cewa, bankunanta basu fitar da sanarwar da ke bayyana 15 ga wata a matsayin ranar daina amfani da tsoffin kudin ba.
Har ila yau, ta ce ba su samu labari a gidajen rediyo, talabijin ko jaridu cewa za a ci gaba da karbar tsoffin kudin har zuwa wani wa’adi ba.
Ba a Abuja ne kadai a ke kin karbar tsoffin kudi ba, ‘yan kasuwa da yawa a wasu jihohi sun daina karbar tsoffin kudaden duk kuwa da umarnin kotun koli.
Alhaji Muhammadu Adamu, wani mai shagon atamfa a babbar kasuwar Gombe ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa, ba yadda zai yi dole ya daina karbar tsoffin kudi.
A cewarsa:
"Tsoro na kada na je banki a ki karba. Maganar na kai CBN kuma bata taso ba, shiga cikin CBN ba karamin aiki bane, ga tsaro, wane irin layi kake tunanin za a yi a can?"
An rufe kanti a jihar Kano
A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnatin jihar Kano ta garkame wani kantin siyayya bisa daina karbar tsoffin kudi.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kotun koli ta bayyana za a ci gaba da karbar kudin har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu.
Karancin Naira: Gwamnatin Jihar Neja Ta Bi Takwarorinta Na Kogi, Kaduna Da Zamfara, Ta Maka Buhari a Gaban Kotu
Gwamnonin Arewa sun maka gwamnatin tarayya a kotu bisa zargin kawo tsaiko ga tattalin arzikin kasa bayan kawo sauyin fasalin Naira.
Asali: Legit.ng