Masari Ya Umurci Bankuna Da Yan Kasuwa Da Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi
- Gwamnatin Katsina ta umurci bankuna da su ci gaba da karbar tsoffin takardun Naira a jihar
- Gwamna Aminu Masari ya kuma umurci yan kasuwa a Katsina da su ci gaba da karbar tsoffin N1,000, N500 da N200 daga wajen abokan cinikinsu
- Masari ya umurci al'ummar jiharsa da su mutunta tare da bin wannan doka don tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya umurci dukkanin bankuna da yan kasuwa a jihar da su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 yayin hada-hadar kudi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa daga kwamishinan labarai, al'adu da harkokin cikin gida na jihar, Yanaya Sirika, AIT.live ta rahoto.
Dalilin da yasa Masari ya bayar da umurnin
Masari ya yi bayanin cewa umurnin ya biyo bayan sanarwar da ministan tsaro kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami ya yi cewa gwamnatin tarayya za ta mutunta hukuncin kotun koli kan sabbin Naira.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotun koli dai ta bukaci a dakatar da wa'adin daina amfani da tsoffin kudi da aka sauya har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun 2023 don yanke hukunci kan lamarin.
Masari ya kuma umurci dukkanin bankuna da yan kasuwa a jihar da su mutunta dokar sannan su ci gaba da harka da duk wanda ya kawo tsoffin kudi.
Gwamnan ya kuma bukaci kowa ya bi wannan umurni don tabbatar da zaman lafiya, aminci da kwanciyar hankali a jihar, rahotpon allnews.
Gwamnatin Kano ta rufe kantin siyayya saboda rashin karbar tsoffin kudi
A wani labarin kuma, mun kawo cewa hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki na jihar Kano ta rufe kantin Wellcare bayan hukumar kantin sun ki karbar tsoffin kudade daga wajen kwastamomi.
Karancin Naira: Gwamnatin Jihar Neja Ta Bi Takwarorinta Na Kogi, Kaduna Da Zamfara, Ta Maka Buhari a Gaban Kotu
Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya yi umurnin rufe shagon kamar yadda mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Danagundi ya bayyana a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu.
Gwamnan dai ya fito fili ya nuna adawarsa da wannan sabon manufa na CBN wanda ya ce ya jefa al'umma cikin hali na kangi da matsi a rayuwa. Harma ya ce gwamnatin Kano basa tare da gwamnan na CBN.
Asali: Legit.ng