Tsoro da Firgici a Zukatan Jama’ar Binuwai Bayan Helikwafta na Sauke Wasu irin ‘Sojoji’

Tsoro da Firgici a Zukatan Jama’ar Binuwai Bayan Helikwafta na Sauke Wasu irin ‘Sojoji’

  • Jama’a mazauna yankin Onyagede a jihar Binuwai sun koka kan wani jirgin sama da ke ta sauke wasu irin jama’a da kayan sojoji amma a mitsike
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa wani Soja mai ritaya a yankin yace ba sojoji bane bayan ganin jama’ar masu hada tsoro da kawo fargaba
  • Sun roki jami’an tsaro sun dasu hanzarta bincikar jama’ar ganin cewa akwai yuwuwar karantsaye kan lamarin tsaro a yankin

Gwamnatin jihar Binuwai a ranar Lahadi ta bayyana tsoron da jama’a mazauna yankin Onyagede da ke karamar hukumar Ohimini suka shiga bayan saukar wani jirgi Mun sama wanda ke cigaba da sauke wasu irin mutane da ke sanye da kayan sojoji amma kuma babu tsafta a yankin.

Taswirar Benue
Tsoro da Firgici a Zukatan Jama’ar Binuwai Bayan Helikwafta na Sauke Wasu irin ‘Sojoji’. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai bada shawara na musamman kan lamurran tsaro ga Gwamnan jihar, Laftanal Kanal Paul Hemba mai ritaya yace jirgin saman mallakin masu hakar kwal ne.

Kara karanta wannan

Canza Fasalin Kuɗi Na Iya Kawo wa Sojoji Tasgaro a Ayyukan su - NSA Monguno

Daily Trust ta rahoto cewa mazauna Onyagede, wani yankin kauye a cikin ranakun karshen mako sun sanar da manema labarai cewa jirgin saman yana ta sauke wasu irin mutane da kayan sojoji.

Mazauna yankin sun zargi cewa, lamarin yana ta tsorata jama’a inda suka roki sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su hanzarta duba yuwuwar barazanar tsaro a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, amma Himba a martanin gaggawa ga damuwar jama’ar Onyagede, ya jaddada cewa akwai bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu don ‘yan sanda da sojoji suna sanya idanu kan dukkan yankunan da ke da yuwuwar fuskantar barazanar tsaro.

Tsohon shugaban karamar hukumar Ohimini, Musa Alechenu, ya sanar da hakan a ranar Juma’a inda yace sai uku a ranar aka sauke sojoji a yankin wanda wani soja mai ritaya da ke zama a yankin ya gane cewa ba sojoji bane.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina Sun Turo Sako Mai Ɗaga Hankali

A daya bangaren, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, Tace rundunar har yanzu ba ta samu bayanan sirri kan harsarin da ke yankin ba daga caji ofis din ta na karamar hukumar.

Mutum 2 sun gurfana a kotu kan zane basaraken yankinsu

A wani labari na daban, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun gurfanar da wasu mutane biyu da suka lakadawa basaraken yankinsu mugun duka.

Ba a nan suka tsaya ba, sun tsare tituna da manyan duwatsu inda suka nemi tayar da tarzoma a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng