Allah Ya Yiwa Mahaifin Gwamnan Jihar Bayelsa, Pa Diri Rasuwa
- Labarin da muke samu ya bayyana cewa, Allah ya yiwa mahaifin gwamnan jihar Anambra rasuwa a yau
- Rahoto ya bayyana cewa, Pa Diri ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, kuma tsohon shugaban makarantar firamare ne
- Majiya daga ahalin ta bayyana cewa, ana ci gaba da shirin jana'iza, za a sanar da lokacin da za a binne shi
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya yi rashin mahaifinsa, Abraham Michael Joseph Diri, Tribune Online ta ruwaito.
Ya zuwa yanzu dai ba a shaidawa duniya sanadiyyar mutuwar marigayi mahaifin gwamnan ba.
A cewar wata sanarwa da Mr. Jothan Diri, a madadin ahalin Diri na Kalama-Owei Wari ya fitar a, an ce dattijon ya rasu yana da shekaru 88 a duniya.
Mr. Jothan ya kara da cewa, ya zuwa rasuwarsa, ya kasance tsohon shugaban makarantar firamare, kuma Kirista mai riko da addini kana mutum abin koyi a cikin al’umma, rahoton Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
“Ahalin Diri da al’ummar Sampou gaba daya sun shaida cewa dan uwanmu kuma mahaifinmu ya yi rayuwa cikakkiya. Za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan kusa.”
Allah Ya Yiwa Dan Sanata David Mark Rasuwa
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Allah ya yiwa dan sanata David Mark rasuwa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A ruwaito cewa, Tunde Mark ya rasu ne a wani asibitin Burtani bayan rashin lafiya da ya yi na dan wani lokaci.
An ce ya kasance dalibin da ya yi shuhura a manyan makarantun kasar nan da ma na kasar waje.
Ya rasu ya bar mata da da daya, kamar yadda rahotanni daga majiyoyi da yawa suka bayyana a lokacin rasuwarsa.
Allah ya yiwa mahaifiyar Ghali Na'Abba rasuwa
A wani labarin kuma, Hon. Ghali Umar Na'abba ya yi rashin mahaifiyarsa shekarar 2022 da ta gabata bayan rashin laifiya da ta yi.
Ghali ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai a Najeriya, inda ya rike kujerar a zamanin mulkin Obasanjo daga 1999 zuwa 2003.
Yayin jana'izar baiwar Allahn, an ga jiga-jigan siyasar kasar nan daga bangarori daban-daban, ciki har da gwamnoni, sanataoci, 'yan majalisu da dai sauran masu fada a ji na Najeriya.
Asali: Legit.ng