Karancin Kudi Ya Sa Tsoho Ya Tafi Banki da Gado, Ya Nemi a Bashi Kudadensa
- Wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta na wani tsoho da ya shiga bankin KeyStone da gado ya jika zukatan jama’a
- A bidiyon, an ga mutumin ya ajiye gado a kasa ya kwanta yayin da mutane ke masa kallon tausayi a farfajiyar bankin
- Jama’ar kafar sada zumunta sun kadu da ganin yadda mutumin ke cikin tashin hankali na rashin lafiya, sun nemi a biya masa bukatarsa
Wani dan Najeriya mara lafiya ya shiga tashin hankali, ya dauki mataki don ganin bankin KeyStone sun dauki kudinsa sun bashi.
A wani bidiyo mai taba zuciya da aka yada, dattijon ya tafi banki da gadonsa, inda ya zauna zaman jira dirsham a harabar bankin.
Ya roki ma’aikatan bankin da su taimake shi su ba shi tsabar kudi domin ya biya kudaden jinya da yake yi a asibiti.
A bidiyon da aka yada a TikTok an rubuta:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ya kamata bankin Keystone ya sake masa kudinsa. Bai shi da lafiya kuma yana bukatar kudi don kula da kansa.”
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
Ga kadan daga masu nuna jimami da tausaya dattijon:
@arnoldatkinson85:
"Na gaza gane wannan nahiya ta Afrika mutum ya zo ciki da kansa ba zai cire kudin da ya sha wahala ya samu ba.”
@jerrygodspower:
"Haba don Allah babu bukatar kawo wannan mutumin nan, cikin sauki ku sauke manhajar Keystone sai ku yiwa asibitin da yake jinya tiransifa.”
@williamkelvin680:
"Na gaji da wannan kasar, ka samo kudi ka karbe su ya zama yaki gwamnati sai mugunta sun manta za su hadu da Allah.”
@realgoa:
"Wannan wane irin matsala ne. Mutanen da ke kusa dashi ya kamata su taimake shi, a ina wannan tsohon yake?”
@imani_quest:
"Idan aka ce musu su saka mutumin da ya dace a aiki, sai suce maka ba dan uwansu bane. Yanzu kowa zai shiga taitayinsa.”
Akwai kudi a CBN, bankuna sun ki zuwa dauka, cewar babban banki
A wani labarin kuma, bankunan Najeriya ne masu laifi idan ana magana kan yadda karancin kudi yake kara ta’azzara a kasar nan.
Wannan na fitowa ne daga babban banki, inda yace bankunan sun ki zuwa daukar sabbin kudaden da aka buga kwanan nan.
A bayyane yake, bankuna a Najeriya na ba ‘yan kasar wahala wajen samun wadatattun sabbin kudade, tsoffin ma sun kare a hannun jama’a.
Asali: Legit.ng