Yan Kasuwa Sun Jinjina Wa Matawalle Saboda Bada Umurnin Kama Mutanen Da Ke Kin Karbar Tsaffin Naira

Yan Kasuwa Sun Jinjina Wa Matawalle Saboda Bada Umurnin Kama Mutanen Da Ke Kin Karbar Tsaffin Naira

  • Kungiyar yan kasuwar yankin arewa sun bayyana goyon bayansu ga umurnin da gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya bada na kama wadanda ba su karbar tsaffin naira
  • Matawalle ya bada wannan umurnin ne bayan umurnin da kotun koli ta bada na dakatar da babban bankin Najeriya, CBN, daga haramta amfani sa tsaffin naira daga ranar 10 ga watan Fabrairu
  • Alhaji Yusuf Nufawa, shugaban matasan kungiyar ya ce matakin da Matawalle ya dauka zai farfado da kasuwanci kuma duk wanda baya goyon bayan hakan yana kan kuskure ko son kai

Sokoto - Kungiyar hadakar yan kasuwar arewa ta goyi bayan umurnin da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bawa jami'an tsaro na kama duk wanda ya ki karbar tsaffin naira yayin kasuwanci.

Yan kasuwan sun jinjina wa umurnin na Matawalle a ranar Asabar a jihar Sokoto, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Ya Fusata, Ya Umarci a Kama Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin Kuɗi

Matawalle
Yan Kasuwa Sun Jinjinawa Matawalle Saboda Bada Umurnin Kama Mutanen Da Ke Kin Karbar Tsaffin Naira. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Punch ta rahoto cewa Matawalle da gwamnonin Kaduna da Kogi ne suka kai gwamnatin tarayya kara a kotun koli, suna neman tsawaita wa'adin cigaba da tsaffin N200, N500 da N1000.

Kotun kolin, a hukuncinta na ranar Laraba ta dakatar da CBN daga aiwatar da hana karbar tsaffin kudin daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kungiyar yan kasuwa ta ce cigaba da amfani da sabbi da tsaffin nairan zai kawo wa al'umma sauki

Shugaban matasan kungiyar, Alhaji Yusuf Nufawa, ya ce za a iya farfado da kasuwanci ne idan shugabanni sun dauki matakai da suka dace na tabbatar mutane na amfani da sabbi da tsaffin takardun nairan kamar yadda Matawalle ya umurta.

Ya ce hakan zai taimaka wurin saukaka wahalhalun da talakawan Najeriya ke sha saboda karancin sabbi da tsaffin takardun nairan.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

Ya bayyana cewa cigaba da amfani da tsaffin nairan da janye su a hankali yayin da ake gabatar da sabbin zai saukaka wahalan da mutane ke sha.

Duk wanda baya goyon bayan matsayar Matawalle yana kan kuskure ko son kai, Nufawa

A cewarsa, ya gamsu cewa wadanda ba su goyon bayan matsayar Matawalle da nasararsa a kotun koli suna kan kuskure ne ko kuma siyasa suka saka a gaba.

Dan kasuwan ya kuma yaba wa gwamnan saboda jajircewa kan abin da mutanensa ke so a maimakon wasu da ke amfani da wahalar mutane don siyasa.

Ya kuma jinjinawa majalisar magabata saboda matakin da suka dauka na umurtar CBN ta buga sabbin takardun naira duba da wahalar da mutane ke fuskanta.

A bangare guda, Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya shima ya jinjinawa Gwamna Matawalle da sauran gwamnonin da suka shigar da FG da CBN kara kan wa'adin dena amfani da tsaffin nairan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Da Sharadi 1: Majalisar Magabata

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164