Jerin Wadanda Suka Halarci Zaman Majalisar Magabata Ranar Juma'a
Shugaba Muhammadu Buhari a yau Jum'a ya jagoranci zaman majalisar magabata da dukkan masu ruwa da tsaki na kasa domin tattaunawa kan abubuwa biyu da suka shafi Najeriya.
Majalisar ta tattauna kan lamarin zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni.
An ji ta bakin shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, kan shin ya shiryawa zaben?
Farfesa Mahmoud ya ce lallai shirye suke, a cewar Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.
A bangaren Sifeto Janar na yan sanda kuwa, an tambayesa shin wani irin shiri suke don tabbatar da tsaro lokacin zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Malami, IGP Alkali ya ce suma shirya suke.
Game da lamarin Naira kuwa, mambobin majalisar sun ce ba yu adawa da sauya fasalin Naira amma gwamnan CBN ya buga isassun sabbin kudi ko kuma ya fito da tsaffi mutane suyi amfani.
Ga jerin wadanda suka halarci wannan zama
Wadanda suka halarta a mutum:
- Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Yakubu Gowon
- Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar
- Tsohon shugaban kasan Goodluck Jonathan
- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan;
- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila
- Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna
- Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno
- Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello;
- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha;
- Antoni Janar kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami
- Gwamnan bankin CBN Godwin Emefiele
- Shugaban hukumar INEC, Mahmoud Yakubu
- Hafsun Sojin dake wajen:
- Shugaban hafsun tsaro, Janar Lucky Irabor
- Shugaban hafsun sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya
- Shugaban hafsun sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo
- Shugaban hafsun sojin sama, AVM Ishiaka Amao
- Sauran hukumomin tsaro:
- IGP na yan sanda, Baba Usman Alkali
- Kwamandan NSCDC, Dr Ahmed Abubakar Audi
- Tsohon Shugaban Alkalan tarayya, Belgore
- Tsohon Shugaban Alkalan tarayya, Mahmud Muhammad
- Shugaban ma'aikatar gwamnati, Yemi Esan
Wadanda suka halarta ta yanar gizo:
- Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Olusegun Obasanjo
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun
- Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa
- Gwamna Yahaya Bello na Kogi
- Gwamna Atiku Bagudu (Kebbi),
- Gwamna Dapo Abiodun (Ogun),
- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto
- Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Plateau
- Mataimakin gwamnan Nasarawa
- Mataimakin gwamnan Bauchi
Asali: Legit.ng