An Nada Wa Dan Atiku Abubakar, Aliyu, Sarautar Turakin Adamawa
- Yayinda mahaifinsa ya dukufa wajen neman shugabancin Najeriya a karkashin inuwar PDP, an bai wa Aliyu Atiku Abubakar sarautar gargajiya a jiharsa ta Adamawa
- Mai martaba, Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa ya nada Aliyu Atiku a matsayin Turakin Adamawa
- Jama'a a soshiyal midiya sun taya matashin murnar wannan sarauta da ya samu, inda da dama suka yi masa fatan alkhairi
Adamawa - Masarautar Adamawa karkashin jagorancin Mai Martaba Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, ta nada Aliyu Atiku, sarautar Turakin Adamawa.
Aliyu na daya daga cikin 'ya'yan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.

Asali: Twitter
Atiku da kansa ne ya sanar da labarin nadin dan nasa a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairu, inda ya taya shi murnar wannan sarauta da ya samu.
Ya kuma roki Allah da ya kare sabon Turakin Adamawa tare da yi masa jagoranci a wannan mataki da ya kai a rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta a shafin nasa:
"Ina taya dana, @AliyuAtiku, murna kan nada shi da Mai Martaba Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa, ya yi a matsayin Turakin Adamawa. Allah Madaukakin sarki ya kare sabon Turakin Adamawa tare da yi masa jagora. Amin. -AA."
Jama'a sun yi martani
@babasaiduJnr ya yi martani:
"Madara mai kama da nono."
@junior_pariya ya yi martani:
"Ma Sha Allah ina tayaka murna AAA."
@yaronatikune ya rubuta:
"Masha Allah❤️ ina tayaka murna dan uwa @AliyuAtiku Allah ya tayaka riko. . ."
@MSailoh ya ce:
"Amin waziri baban turaki baban Nigeria✊"
@Bakisaeed ya ce:
'Allah ya tsanya alkhairi."
@jauroone ya ce:
"Allah kama masa Ameen."
@muhammadmk01 ya ce:
"Masha Allahu."
@IBNAN44 ya ce:
"Allah Taya shi riko."
@MFagwalawa ya ce:
"Ameen ya hayyu ya qayyum."
@BolajiJimba ya yi martani:
Ina taya sabon Turakin Adamawa murna Barakallaufih."
@Husaini_usman66 ya yi martani:
"Maa'Shaa'Allaah AlhamduLillaah BarakalLaah. Ina taya shi murna. Allah Ya qara daukaka, ameen."
'Ya'yan PDP 8,000 sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kwara
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta yi rashi na dubban mambobinta a jihar Kwara inda suka fice zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasar.
Masu sauya shekar sun sha alwashin tabbatar da nasarar dukkanin yan takarar APC a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng