2023: Malamin Addinin Kirista Ayodele Ya Bayyana Wahayin Wani Babban Hatsari A Gaba, Ya Gargadi Yan Najeriya

2023: Malamin Addinin Kirista Ayodele Ya Bayyana Wahayin Wani Babban Hatsari A Gaba, Ya Gargadi Yan Najeriya

  • Primate Elijah Ayodele ya sake bayyana wani abu da ya hango zai faru bayan babban zaben 2023
  • Malamin addinin ya bayyana cewa akwai karin wahalhalu a gaba kuma duk wanda ya ci zaben ba zai iya yin wata siddabaru don magance matsalolin kasar ba
  • Ayodele ya yi gargadin cewa dole yan Najeriya su yi zabe cikin hikima kuma ya yi kira ga INEC kada ta bawa yan Najeriya kunya

Primate Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya ce kada yan Najeriya su yi tsammanin wani surkulle daga wanda zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Osho Oluwatosin, mai magana da yawun malamin addinin, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa Legit.ng a ranar Alhamis 9 da watan Fabrairu.

Primate Ayodele
2023: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Wani Babban Hatsari Da Ke Gaba, Ya Gargadi Yan Najeriya. Hoto: Primate Elijah Ayodele
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fadi Wanda Zai Zama Babban Kalubale Wajen Shirya Zaben 2023

Abin da Primate Ayodele ya ce game da sakamakon zaben 2023

Malamin a sabon abin da ya ce ya hango ya bukaci yan Najeriya su zama cikin shiri domin akwai karin shan wahala a gaba bayan zaben shugaban kasa na 2023, ya kuma ce wasu yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, za su dagula al'amura.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Akwai wasu 'kabal' da za su fitini gwamnatin Buhari saboda lalata masa gwamnati. Jam'iyyar APC ce za ta lalata gwamnatin Buhari. Ba mu riga mun ga wahala ba, abin zai munana idan muka zabi wanda bai shine ya dace ba."

Abin da ke faruwa baya-bayan nan game da Primate Ayodele, Hasashen 2023, Zaben 2023, INEC

A cewar Primate din, ya zama dole hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi takatsantsan don kada ta jefa kasar cikin babban rikici.

Ya kara da cewa yan Najeriya sun dogara ne da hukumar zaben kuma duk wani abin zargi daga INEC zai iya janyo bore a kasar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya warware zare da abawa ga shugaban INEC kan sabbin Naira

Don haka Ayodele ya shawarci shugaban INEC, Mahmood Yakubu, kada ya yi gaggawar sanar da wanda ya lashe zabe don kudin kuskure da zai iya lalata goben yara masu tasowa.

Malamin addinin kirista ya ce an masa wahayi cewa Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari

A yayin da ake tunkarar babban zaben 2023, fastoci da sauran malaman addinin kirista sun yi babban taro addu'a na mutane miliyan daya domin fatan cikar burin shugabancin kasa na Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164