Abin da ya sa Aka Samu N285m a Ajiye – Banki Ya Fadi Dalilin 'Boye' Sabon Kudi

Abin da ya sa Aka Samu N285m a Ajiye – Banki Ya Fadi Dalilin 'Boye' Sabon Kudi

  • Bankin Sterling ya yi magana a game da zargin samunsu da laifin boye fiye da Naira Miliyan 280
  • A wani raddi da bankin ya yi wa Hukumar ICPC a Twitter, ya ce ba haka gaskiyar lamarin yake ba
  • Wani jami’in bankin yake cewa an tara kudin a wurin ne da nufin a rabawa sauran rassoshinsu

Abuja - Bankin nan na Sterling, ya wanke shi daga zargin da hukumar ICPC ta ke yi masa na boye makudan miliyoyin sabon kudin da jama’a suke nema.

A wani karin haske da bankin ya yi a shafinsa na Twitter, ya ce zarginsu da boye sababbin kudi a babban ofishinsu da yake birnin Abuja ba daidai ba ne.

Legit.ng Hausa ta fahimci a yammacin Laraba ne bankin ya fitar da jerin raddi ga hukumar ICPC a dandalin Twitter a kan abin da ya faru a makon nan.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: El-Rufai ya fadi abu 1 da gwamnoni 36 suka roki Buhari ya yiwa talakawa

Bankin ya ce jawabin da ya fito daga hukumar ICPC zai iya rudar da jama’a, kuma ba daidai ba ne. Jaridar nan ta The Cable ta fitar da wannan rahoto dazu.

Mu na bin dokokin CBN - Sterling

Kamar yadda bankin ya yi karin bayani a dandalin na Twitter, yana bin duk sharuda da ka’idoji da babban banki na CBN ya gindaya a kan sababbin kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar bankin, a lokacin da jami’an ICPC suka kawo samame zuwa ofishinsu da ke garin Abuja, ana raba sababbin kudi a duka na’urorin ATM da ke nan.

Banki
Bankin Sterling a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bugu da kari, bankin ya ce abokan huldarsu su na cire kudi a cikin banki kamar yadda Gwamnan babban banki, Mista Godwin Emefiele ya bada umarni.

A rahoton Daily Trust, an fahimci cewa bankin na Sterling su na ikirarin miliyoyin da aka samu ba na su ba ne, suka ce ba su yin aiki da marasa gaskiya.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Bidiyon yadda wasu 'yan Najeriya ke dafa taliya a banki yayin bin layin ATM

Bankin na mu matattara ce - Jami'i

Rahman Owodeyi ya ce a reshen bankin da aka samu kudin ne ake tara kudin da za a rabawa sauran bankunansu da ke Utako, Wuye, Kontagora da majalisa.

Ranar Talata da ta wuce ne jami’an hukumar ICPC suka dura bankin har suka cafke manajojinsa da manyan jami’ansu bisa zargin sun boye sababbin kudi.

Daga baya an saki wadannan ma’aikata ta hanyar beli, amma aka cigaba da gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng